Breaking News

Diddigar Kaya 2


 DIDDIGAR ƘAYA 

   (Mai Wuyar Tsincewa)


بسم لله الرحمن الرحيم 


FATIMA MUHAMMAD GURIN.             

         (Gureenjo)


ADABI WRITERS ASSOCIATION 


Marubuciyar:

*Zuhraa*

*Hamrah*

*Igiyar Rayuwa*

*Noor Iman*

*Ruwan Sama..*

*Lelewal*

*GAMON JINI paid*

*Kowa Ya ga zabuwa..*

And Now..

*Diddigar ƙaya... Paid*


                      *Shafi Na Biyu*


*PAID BOOK*


ÆŠANÆŠANO


**Wannan shafi gabaÉ—ayanta sadaukarwa ce gareki sister zainab Salis, hausawa suka ce yaba kyauta tukuici na ji daaÉ—i sossai da wannan kyauta Allah ya saka da alkhairi🥰❤️**


Ba'a samu kan Fauza ba har Seda aka nemi doctor da kyar ta farfado, in ka ganta bazaka ce Fauzan Jaddah ba ce gabaɗaya ta firgice wadda hakan ya taɓa zuciyar Jaddah da Baba prof sossai.


Ya sani auren dole a musulunce haramun ne, sede yana da tabbacin gata ya musu wadda har abada ba zasu mance ba, watarana kuma in sun tuna zasu yi alfahari dashi su mishi Adu'a idan har be riski lokacin da rai ba, sannan sunan gidanshi ya riga ya fara ɓaci ta silar Fauziyya har hawaye ya zubar saboda wani da ya tare shi ya faɗa mishi magana marar daaɗin ji akan ɗiyar ƙanin nashi, sannan ya san halin Fauziyya ba me chanzuwa da sauki bane muddin bata gamu da abunda ya girgiza mata kwakwalwa ba, ko ta shiryu samun mijin da zata samu farin ciki da kaunar en uwanshi ze yi matukar wahala hankalinsu baze taɓa kwanciya da tayi ta musu yawon makaranta alhali sun san da cewa ga hanyar da ta ɗauka ba.


Duk zaune suke a babban parlorn nashi, in ka cire yara daga kan Fa'iza dake sa'ar Fauziyya zuwa kan auta Faazila babu wadda babu a wurin kuma tsab ya É—auke su duka har ya bar fili me yawa saboda girman parlorn na Baba prof.


Gyaran murya yayi kan ya fara nasiha me ratsa jiki akan bin umarnin iyaye da kuma kyautata musu, daga nan ya ɗaura da haƙuri da irin girmansa har a wurin Mahalicci, bayan ya gama ya kira sunan Fatima.


ÆŠago rinannun idanunta da suka haÉ—u da fuskanta suka kumbure tayi ta kalleshi kan ta maida kanta Æ™asa tana bitar karatun da ba'a jima da fara É—aura mata ba tace 

"Na'am Baba"


Yace 

"ke zan fara ba haƙuri Fatima, na san mun miki ba daidai ba kina zaman zamanki mun saka mijinki aure, amma ki sani mu ɗin ma bamu isa hakan ta kasance ba idan ba da yardar Allah da sahalewarsa ba, Ke da Fauziyya ƴan uwa ne waenda kuka tashi gida ɗaya ɗaki guda kusan gabaɗaya rayuwarku tare kuka yi shi, babu halin juna da baku sani ba hakan yasa nake jan kunnen ki da ki cigaba da rike Fauziyya a matsayin ƙanwarki, kiyi haƙuri da duk wasu halayen ta kaman yadda na san ki na kuma shede ki me dumbin haƙuri da kauda kai, to ki ƙara akan hakan, Allah ya zaunar daku lafiya ya baku zuri'a dayyaba"


Kanta Æ™asa hawayenta da ta kasa rikewa na É—iga akan shinfidadden jan carpet da ya cike parlorn tass tace 

"in shaa Allahu Baba, ai Fauziyya ƙanwata ce kaman yadda ba zan iya cutar da Fa'iza ba haka ba zan taɓa iya cutar da Fauziyya ba, Zaku sameni me hakuri akan hakan Allah ya bamu zaman lafiya"


Kowa a parlorn seda ya sa mata albarka, Fauziyya wani irin baƙin ciki ya zo mata wuya, a duniya in akwai abunda ta tsana ya biyo bayan munafurci wallahi ita bata taɓa yiwa Fatima kallon ba munafuka ba, komai nata na munafurci ne, sunanta da Baba prof ya kira ne ya katse mata bitar wasiƙar jaki.


Ta É—ago fuskanta da yayi mugun chanzawa ta kalleshi.


Yace 

"Fauziyya ba wai Bama son ki bane muka nace da lallai se an É—aura wannan aure, ina so ki san gata ne wadda ba kowa ke samun irin wannan ba, Fauziyya ke ce shaye shaye kece club club da hotels hotels babu wani zuri'a da zasu zauna dake ba tare da sun wulakanta ki ba..."


Katse shi tayi saboda yadda zuciyarta ke matukar ƙuna idan aka jefeta da waennan kalamai masu daci wadda ta san ba laifin kowa bane illa nata.


Hawaye na gangaro mata ta miÆ™e tsaye tace 

"Duk nan kuna zargi na ne da zina da kuma kuma shaye shaye, lallai idan har kuna zargina ku dangi na waenda na É—auka bani da ya su a duniya to babu wadda ze yarda dani kuma!"


Katseta babanta yayi yace 

"Me yasa baki da kunya ne ni kam a rayuwarki Fauziyya? Kin zauna kin rufewa mutane baki ko se na zo nan nayi fata fata dake?"


Baba prof ne ya dakatar dashi ya san she's too young for all this duk tauna tsakuwar da suke don kawai aya taji tsoro ne.


Yace

"kina nufin ki ce duk wasu videos da hotuna naki da aka turo mana ƙarya ne? Ko kuma ganinki sau biyu da Faizan yayi a mabanbanta hotels da mutanen banza cikin shigan banza da buguwa suma ƙarya ne? Ko ganinki da idanuna da nayi shima karya na miki? Ko kuma biyo cikin layin nan da kika yi a buge shima karya ne?"


Girgiza kai tayi in confused tace 

"bani da masaniya akan wasu pictures da videos, shi kuma da ya ganni duk a wuraren na yarda ni ya gani amma na rantse da wanda raina yake hannunsa ban taɓa aikata zina ba, tun da nayi wayo na san menene zina kuma na kyamaceshi wallahi ban san duk yadda abubuwan suka zama haka ba..."


"FAUZIYYA!"

Yayanta Farhan ya kirata yace cikin jin zafinta 

"Ki dena rantsuwa akan ƙarya zaki cutar da kanki da kanki!"


Shesheka ta ja me karfi tana ciccilla idanunta cikin parlorn, chan cikin sif É—in baba prof ta hangi Alqur'ani izu sittin da gudu taje ta É—auka tare da É—aurawa akai

 a razane duk suka miÆ™e suna kallonta har Faizan da duk jijiyoyin jikinshi suka miÆ™e saboda wani irin tafasa da zuciyarshi ke yi, ji yake kaman in ya kamata da musu da rantsuwar nan ze iya kashe ta.


"Na rantse da wanda ya saukar da wannan littafi ban taɓa aikata zina ba kuma ban taɓa ɗaga abun maye da hannuna cikin hayyacina na sha ba, ban san meke faruwa dani ba amma wallahi ko a mafarki ban taɓa aikata zina...."


Kwace Alqur'anin da aka yi a hannunta ya sakata saurin É—agowa se suka HaÉ—a idanu, yana shirin sauke mata zazzafar mari mahaifiyarshi tayi Charab ta riÆ™e hannunshi a kausashe tace 

"A kul Faizan! ban yarda ba ban amince ba, ko a bayan idanunmu ka daga hannu da sunan dukan Fauziyya ban yafe maka ba duniya da lahira!"


A razane yake kallon mahaifiyar tashi kan yayi wani magana mahaifinta ya bata mari daya, Farhan ya ƙara mata har Seda bakinta ya fashe.


Da sauri Amminta ta miƙe ta nufi kofa tana kuka, Baba prof ne ya dakatar da ita

"Ruƙayya!"


Tsayawa tayi tana jin yadda kukan É—iyarta ke ratsa parlorn.

"Dawo ki zauna"


Mikewa ya yi da kanshi ya nufi Fauziyya ya riƙe hannunta suka dawo dab dashi a ƙasa ta zauna kanta ƙasa tana cigaba da kuka.


Kallon su yayi É—aya bayan É—aya kan ya sauke ajiyar zuciya yace 

"Farhan ban yarda ba ko da bakin wasa ka sake ɗaga hannunka akan Fauziyya, bana so ka sake mata kallo a matsayin ƙanwarka ita ɗin matar yayanka ce a halin yanzu"


Hannunshi na kan ta yana shafawa ya ɗaga ya kalli Faizan da da kallo guda zaka san ranshi be taɓa sosuwa irin na ranar ba, ko ɗagowa baya yi yadda mamminshi ke fifita wannan yarinyar fiye da farin cikinshi hakan na matukar ƙona ranshi, idan ya kalli matarshi da halin da ta shiga duk saboda ita se yaji ina ma ze iya kawar da ita a duniya ko ze huta.


ÆŠauke kai baba prof yayi shima kwarai ya san an shiga hakkin shi sede ya za'ayi shine babba dole shine Juji.

"Fauziyya ki sani yanzu bakin alƙalami ya riga ya bushe, duk wannan bashi da anfani sannan Qur'ani ya wuce wasa babban hatsari ne amfani dashi wurin rantsuwa se idan har babu yadda za'a yi ne.... Ki yi haƙuri ki rungumi sabuwar rayuwar ki"


Kai ta gyaÉ—a tace

"shi ke nan Baba"


Shafa kanta yayi yace

"Allah ya miki albarka"


Babanta yace 

"Ni kam ba zan ce kiyi hakuri ba, in kin ga dama kar kiyi abunda nake so ki sani shine daga ranar da kika kashe aurenki karki neme hanyar gidan nan, kije chan wurin abokanan watsewarki ku cigaba na yafe ki har Abada, in har kina son Adu'a da farin cikina gareki shi ne ki zauna da Faizan ba tare da wani matasala ba, ko a labari na ji ranar da kika saɓawa umarninshi Fauziyya ban yafe ba, tun rayuwarki baki taɓa saka ni farin ciki ba kullum da fargabar abunda ze fito daga gareki nake kwana nake tashi, sau ɗaya dae zaki yi kokarin proving Cewar ke ɗin ɗiyata ce har ki min biyayya!"


Ammi ta É—ago tana Kallonshi

"me yasa ne Sulaiman? Me yasa kullum ka buɗi baki alkhairi baya fita in har dae akan Fauziyya ne? Duk wannan hali da ta shiga da wadda take ciki baka taɓa tausayinta ba! Ni kam wlh ban yarda a zalunce ta ta ja baki tayi shiru ba!"


Kallonta kawai jadda ke yi, wani lokacin hankalin Ruƙayya na bata mamaki ganin idanunta tana ga yadda Aisha da Prof ke ture yaronsu ba wai don basa sonshi ba se don ganin sun samawa Fauziyyan ƙima da daraja a idanun Faizan ɗin sun kuma hana shi cutar da ita saboda rashin ƙaunarta da baya yi tun tale tale, amma ji inda ta dosa ita, babu wadda ya fi dacewa yayi magana a nan na rashin adalci irin Fatima da mahaifiyarta amma they sat patiently suna sauraron baba prof ɗin.


"Ruƙayya...."

ÆŠaga mishi hannu baba prof yayi, kan ya dubi Faizan 

"Faizan ga amanata na baka, ka san girman amana ka kuma san hukuncin duk wadda ya ci amana, in ka cutar da ita ina rokon Allah ya saka mata, Allah yayi muku albarka ya baku zaman lafiya, an riga an yi mata jerenta so mutum biyu ne kawai zasu raka ta su dawo"


Mammi tace 

"Toh ka ji, nima Amana na baka Fauziyya in ka ci ma kanka! Ka riga kayi karatu babu abunda baka sani ba, ina fata zaka wanzar da adalci a tsakaninsu su biyun"


Jadda da hawaye suka zubo mata da kewar fauzin nata tace 

"Fauziyya kiyi haƙuri! Kiyi hakuri!! Ki ƙara haƙuri!!! Ina tabbatar miki zaki ci ribar wannan haƙuri.. Faizan ga ƙanwarka nima na damka maka amanarta, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyaba, Fatima kiyi hakuri kin ji? Haka Allah ya tsara"


Kuka sossai duk su biyun suke kowa da abunda yake saƙawa cikin zuciyarsa, Fauziyya ta ƙudiri aniyar zama ɗiya ta gari for the first time ko don saboda Mammi da Baba prof, ko don babanta yayi alfahari da ita sau ɗaya dae a rayuwarta, bata taɓa saka shi farin ciki ba kap rayuwarta se bakin ciki har hawan jini yake dashi sanadiyarta, zata yi hakuri har taga yadda Allah ze yi da ita a wannan gida da yafi kabari ko wuta a gareta....


Kowa yana ta kara yi mata nasiha har suka fito a yammacin zasu tafi Abuja inda nan ne gidanshi kuma anan suke zama da Fatima, bata taɓa Tunanin zata yi wani kukan rabuwa da gidan da tafi tsana ba se yanzu da take ji yafi mata sau dubu akan inda za'a kaita a kuma barta chan bata san kowa ba se maƙiyanta, kuka sossai take yi da kyar aka cire ta ɗaga jikin jadda se ta koma na Amminta, daga nan tayi kan mammi ta sha kuka kam, daga karshe ma fa'iza da kullum se sun yi faɗa ta rungume tana kuka sossai, Fatima tuni tana mota.


Cikin sassarfa ya fito daga sashensu ba tare da ya kalli ko sashen inda suke ba ya nufi mota sanye da wasu É—anyen boyel me taushi da tsada farare sol, hulanshi light ash da fari tangaran ya zauna mishi sossai haka takalmin shi half cover ce me ainihin kyau da tsada ta bayyana Fararen digadiginshi da kaman baya taka kasa.


Baba prof da ya bishi da kallo yana murmushin yadda duk yayi kicin kicin da rai yace 

"Faizan!"


Juyowa yayi se yayi kaman yanzu ne ya kallesu alhali tun fitowarshi ya san suna wurin, nufansu yayi kanshi kasa yace 

"Na'am baba"


Jadda, momma da Baba Alhj duk babu wadda ya fito Amminta kuma ta juya mata baya, da Yaya Fadeelah da wata Æ´ar uwar su Baba prof zasu tafi, Kallonsu yayi yace 

"ku je ku shiga mota ga mijinta ze zo da ita yanzu"


Kanta ƙasa tana shesheka duk masu rakiya suna tsaye cike da tsakar gidan ana ta mata Adu'o'i.


Hannunta baba prof ya riÆ™e ya sanya cikin hannunshi a tare suka É—aga suka kalli baban se suka kalli juna, dukkansu suka É—auke kai, gyalen ta baba prof ya sake ja ya rufe mata goshi yace 

"Allah yayi muku albarka! Allah ya tabbatar muku da farin ciki a wannan tarayya ku je kuna cikin adu'o'inmu a kullum, Fauziyya karki manta duk abunda na ce miki kinji?"


Kai ta gyaɗa, hanya ya nunawa Faizan se ya juya riƙe da ita suka nufi mota, dole ya biye mata suna tafiya kaman ba zasu taka ƙasa ba don haka tafiyar ta, idanun mutane da Baba ya sanya ya saka hannu ya buɗe mata gefen ta shiga ya gyara mata kayan ta kan ya rufe kofar fatima dake gefe ɗaya ta ja tsuka me karfi, gaban motan ya shiga Farhan ya ja suka fice kan na su yaya fadeela ya biyo bayansu.


Basu tsaya ko ina ba se Airport, suna parking ya fita ya shiga ciki yana waya kaman yadda tun da suka fita daga gidan waya yake, Fatima fushi take dashi kaman shine ya ɓarar mata da ciki hakan yasa itama be kula ta ba, yaya fadeela ce ta zo ta riƙeta suka shiga ciki Fatima da Ya kaka suka biyo su cikin mintuna ya gama komai, ya zo ya Mikawa kowa tickets nashi suka wuce suka yi checking suka shiga jirgi.


Banda ajiyar zuciya babu abunda take saukewa, ba wannan ne karonta na farko shiga jirgi ba Dukda duk gidansu babu wadda ya sani sede tana yawan zuwa Abuja da friends nata kuma da jirgi hakan yasa bata ko nuna alamar tsoro ba, jirgin na daidaita a sama ta yaye gyalen ta sbd zafi, daga inda take tana hangar yadda Fatima ta kwanta a jikinshi yana riÆ™e da hannunta da alama rarrashi yake. 


Kau da kai tayi tare da tsaki tana kallon window ta fara Tunanin rayuwata Daki-daki....duk me ya jawo waennan abubuwa da suke faruwa? Shin wacece ita tun daga farkon fari? 

A take tunaninta ya daka tsalle yayi baya daga inda ta fara sanin wacece ita...


DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuÉ—i ne.. 

Ze zo muku a Naira É—ari uku kachal #N300.

Acc no. 0545475847 

Acc name. Fatima Muhammad Gurin 

Bank name. Gt bank

Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin 

09039206763 

Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp.

Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰


Karku sake a baku labari.



               ðŸ–¤Gureenjoh🖤

No comments