Breaking News

Diddigar Kaya 12


 DƘ


12


Daidai tana sanyo kafa shi kuma yana Juyawa, an tambayeshi wani code da se ya duba paper ɗin don be riƙe ba, har ta gama ta wuce seat ɗinta chan karshe be dawo ba.


"Ke kinga wani haɗaɗɗen captain da ya tafi da ni? Wlh ya haɗu karshen haduwa ina ma zan samu ko phone number ɗinshi ne"

Rahama dake kusa da ita ne ke maganan cikin koɗa kyaun wadda take magana a kai da ita bata sani ba.


Tace

"ni ban ga wani captaina ba, kuna da matsala ai ku kam"

Ta faɗa jin sakina ma ta karɓa tana taya rahama gulman wadda bata gani ba ita kam.


Har suka sauƙa yola basu daina maganan captain ɗin nan ba, Sakina Dan Tsoho hotel tayi don chan zata karasa satin da tace zatayi a gida, yayinda rahama tayi gida don duk iyayenta basa ƙasar, cab ne ya sauke ta kofar gida ta sauka tare da miƙa mishi kudinshi ta Janyo loggage ɗinta tayi ciki.


Harabar gidan nasu tsabtsab ba kowa ta tabbatar yanzun haka suna school tunda kwata kwata karfe goma ne na safe, sashen jadda tayi direct a parlor ta taddata kan sallaya ta idar da walaha tana tasbihi, da gudu ta zo ta faɗa jikinta tayi shiru tana sauke numfashi.


Ɗago fuskanta Jaddah tayi cikin farin cikin ganinta tace 

"oyoyo oyoyo! Maraba da mutanen Gombe kune da safen nan?"


Kai kawai ta gyaɗa ta sake mayarwa tayi lamo, Jaddah ta ɗago ta gabaɗaya tana kallonta 

"lafiyan ki kuwa? Ko baki da lafiya ne kike hawaye?"


Hannu ta sa ta share kwallar tare da karya wuya tace a shagwabe 

"kewarki nayi Jaddah na"


Dariya Jaddah tayi tace 

"to ba gashi kin dawo ba? Ba shikenan ba? Oya tashi je kiyi wanka ki sauya kaya bari na sa zaliha ta sama miki abunda zaki ci"


Mikewa tayi ta nufi ɗakinta tana cewa 

"ya yi yaji pls"

Tana shiga ta jefar da Akwatin tare da dogon hijab da daga Airport ta sanyo shi zuwa gidan, ta shige toilet ta sakarwa kanta ruwa tana lumshe idanu, se yanzu take jin wani sukuni na rufe ta, lallai ta zalunci ahalinta tayi fatali da tarbiyar gidansu, tunda ta dawo daidai take jin rashin daaɗi a zuciyarta na abunda ta aikata amma fa wani zuciyar na kwaɗaita mata daaɗin shi.


Bayan ta fito tayi shafe shafenta ta janyo tsarabar da Zubair ya Haɗa ta dashi, chocolates ne daban daban se wasu designers perfume guda biyu se, hoodie ash na kamfanin Fendi.


Boyesu tayi a wardrobe ɗinta kan ta zaro riga ƙarami fari da wando navy blue ta saka, wandon a kaurinta ya tsaya ya kuma matse ta ya fitar da duk wani shape ɗinta, gashinta ta taje ta sake shi, tana shirin kwanciya Call na Zubair na shigowa wayanta, da sauri taje kofa ta rufe da key kan ta dawo ta haye gado tare da shigewa bargo ta amsa.


A hankali suke waya tun bata saki jiki ba har ta sake saboda ya iya hira da sanya dariya ga kalamai, ta shagala sossai se jin bugun kofa tayi da sauri ta ce mai tana zuwa ta kashe wayar tare da boyeta cikin Rigan pillow ta dirka taje ta buɗe kofan.


"Jadda tace ki fito ki ci abinci kar kiyi bacci baki ci ba"

Cewar zaliha.


Bayan zaliha ta bi suka fito tare, kan kujera ta zauna bayan ta ɗauki abincin daga cikin tray da zaliha ta shirya ta fara ci, Jaddah na bata labarin irin kewar ta da suka yi gidan yayi shiru sossai a kwana biyu da bata nan.


"Ashe ana kewata amma in ina nan kowa ya buɗe baki Fauxa kaza Fauxa kaza!"


Jadda zata yi magana wayanta ya fara ruri ta duba tace 

"oh kai kuma se yau ka tuna dani" 

Ko bata faɗa ba Fauxa ta san waye don haka ta maida kanta kan TV Dukda wa'azi ne gwara ta ji da ta ji zancen da zasu yi.


Bata san ma jaddar ta kashe ba saida taji tana cewa 

"Fauziyya yi sauri gama ki je ki sharewa Yayanku ɗaki ki wanke mai toilet yadda kwana biyu be zon nan ba na tabbatar yayi kura kuma kin san shi da rashin son datti, yace min ya shigo garin gida ne dae ze ɗauki mintuna masu yawa kan ya karaso akwai abunda ze yi"


Haɗe gabas da yamma tayi kaman zata yi kuka tace 

"Jaddah ina Fatima da ni zan mishi aikin ɗaki yau? Allah ya kyauta wlh kin dae san kap rayuwata ban taɓa taka kafa ɗakin shi ba haka kawai ba zan fara yau ba..."


"Fitsararriya ajiye abincin nan ki wuce kan in Haɗaki da abincin in take"

Cewar baba Alhj da yake shirin shigowa sallamar da ze yi ma be yi ba sbd abunda yaji Fauzar na faɗawa Jaddah.


Da sauri ta miƙe tsaye 

"ban hanaki saka waennan kayan ba?"


Da sauri ta wuce ɗaki tana tura baki seda ta shiga ta fara kunkuni, kaman zatayi kuka haka ta sanya hijab kato har ƙasa ta fito, ta samu baba Alhj na cewa Jaddah


"Mama ni fa ba tsanar ta nayi ba, halayen ta ne bana so, a yadda Fauziyya ta ɗauko rayuwarta wlh bata so gamawa da duniya lafiya ba, tun da ta sanya kafa ta bar sashena bata sake zuwa ko da gaisheni bane wai dani uban ta zatayi gaba? Har Fauziyya ta bar garin nan bata iya zuwa ta min sallama ba se a bakin mamanta nake ji?"


Kanta ƙasa tace

"key!"


Jadda tace 

"Kin san inda nake ajiyewa ai"


Ɗakin Jaddar ta wuce ta ɗauko ta zo ta fice jin Jaddah na bashi hakuri ta kuma tabbatar mishi da ta tura ta ta mishi sallama saide kila zuwan ne bata yi ba, zata mata faɗa Adu'a da lallashi Fauza ke bukata ba faɗa da duka ba.


Ita kam ta wuce abunta, ita fa a yanzu mahaifin ta bata san wani baabi ta saka shi ba, dukda tana son shi sossai da sossai saide wannan kiyayya da yake nuna mata yasa itama take jin babu ruwanta da shi (Subhanallah).


Direct ɗakin Faizan ta wuce, a hankali ta tura kofan bayan ta murda key ɗin, kamshin room freshner da na turarukanshi ne suka bugeta, inda zata iya jinjina mishi kenan tsabta da kamshi, komai tsab tsab yake a ɗakin Sam babu tarkace kaman ba ɗakin namiji ba.


Gado ne a ɗakin saɓanin sauran ɗakunan samarin gidan dake da katifa, daga gaban gadon akwai set na kujeru se TV manne jikin gini, daga gefe akwai ɗan corridor inda drawer ɗinshi yake se kofar toilet, bedding ta fara cirewa ta chilla cikin kwando wankin dake gefen wardrobe ɗinshi tare da ɗaukan tsintsiya ta fara aikin ɗakin, tana yi tana mita da masifa wlh ba don jadda ba da abunda zata mishi a dakin nan se ya kusa kasheta, sannan itama yanzu tana son lafiyar fatarta inda Allah ya taimake shi kenan.


Tsab ta share ɗakin ta gyara tare da kunna burner ta sa turaren wutar da ta gansu kan dressing mirror ɗinshi masu kamshi irin na asalin Maiduguri, ta kunna Ac take ɗakin ya ɗau kamshi, bayi zata shiga se ta cire hijab ɗinta ta ajiye kan cushion kan ta wuce bayin, komai tsabtsab, wankewa tayi tana yi tana masifa, haka dae ta gama ta nufi fita. 


Tana sanyo kai ɗakin shima yana sanyowa, a kan junansu idanunsu suka fara faɗawa, wani irin disgusting look na me kike min a ɗaki ya fara watsa mata, ita kuma se ta so rikicewa don ko yaya Faizan na da wani kwarjini da babba ma se ya ji wani iri in ya zuba mai idanun nashi bare mace karama irin ta.


Bata saba gaishe shi ba don haka bazata fara yau ba, wucewa Tayi ta ɗau hijab ɗinta zata sanya, se lokacin ya tuna abunda ya gani a Abuja don haka kai tsaye hannunta ya fara bi da kallo, kan ya maida idanunshi kan body shape ɗinta da ya bayyana sossai a wandon kaman yadda ya bayyana a wanchan kayan da ya gani, daga karshe ya kai kan gashin kanta daidai lokacin ta gama sa hijab tare da nufan kofa.


Kai tsaye yace 

"Ke!" 


Chak ta tsaya, ya fara takowa gabanta hannunshi zube bisa aljihun wandon shi.


"Ke! Sa gwiwowinki a ƙasa"


Da sauri ta kalleshi kaman zata fashe da kuka tace 

"Amma me na y...."


Ɓas haka ya buge mata baki da sauri ta dafe bakin yace 

"kin yi abunda nace ko se na tattaka ki?"


Da sauri tayi kneeling ranta duk ya gama ɓaci wani tsanar shi na sake mamayarta.


Shi bai damu da ita ba don haka be damu da ko ta gaishe shi ko bata gaishe shi ba, clearing thoughts ɗinshi kawai yake son yi..

"Me ya kaiki Abuja?"..


Rassss haka gabanta yayi wani irin mummunan faɗuwa, hannayenta suka soma rawa, bata ɗago ba don tana ɗagowa firgicin idanunta tsab ze bayyana rashin gaskiyarta.


"Don't let me repeat myself... Uban me ya kaiki Abuja? Me kika je yi a Transcorp Hilton?"


Gabaɗaya wani irin zafi ne ya rufe ta kaman an sanya ta cikin Kasar tukuban tsire 

"A...abu...ja kuma?"


Be yi magana ba, tace da sauri

"ni babu abunda ya kaini Abuja, ban je Abuja ba"


Duk yadda ya so ya firgita ta ta faɗi gaskiya be samu nasara ba sbd ta kafe kai da fata ita bata je Abuja ba.


Tsaki me karfi ya ja yace 

"get out of my sight"


Da sauri ta miƙe tayi kofa ya sake cewa.

"Ke!"


Chak ta tsaya, yace 

"this is the last time da zan ga waennan singallin kafafun naki a ɗakina bana son harka da kazamai kin gane ko?"


Kai ta gyaɗa wani irin takaici na zuwar mata wuya, duk Jaddah ce ta ja mata.


Da sauri ta fice tayi sashen Jaddah kaman zata fashe don fushi da tashin hankali.

Taya aka yi Ya Faizan ya ganta a Abuja?  Allah ka rufa min asiri.

Ta furta tana me shiga parlorn Jaddah har zata wuce jadda tace 


"Fauziyya"

Dawowa tayi tana amsawa ganin jaddar is serious.

"Fauziyya kin san girman iyaye ko? Kin kuma san saɓawa iyaye kaman saɓawa mahallicci ne ko? Sannan kina gani irin yadda mahaifanki basu saɓa mini ba meyasa kike shirin daukar wani hanyar saɓa musu alhali ban koyar dake ba?"


Raurau tayi da idanu tace 

"me nayi kuma Jaddah?"


"Meyasa zaki yi tafiya baki sanar da mahaifin ki ba? Ba wannan ba meyasa tunda kika dawo nan baki je kin gaida shi ko sau ɗaya ba? Kina son ganin haske a rayuwarki? Ya kamata ace kiyi nadama ki shiga alhini akan korar da yayi miki a sashenshi amma Fauziyya duk babu? Ko don kinga kina dani? Har fa rashin lafiya mahaifin ki yayi cikin wata biyar din nan ashe baki je kin gaishe shi ba?"


Bakinta kaman ze taɓa gini tace 

"amma Jaddah kina ji yace ko ganina baya son yi, taya zan kai mishi fuskar da baya son gani da sunan gaisuwa?"


"Fauziyya!"

Jaddah ta kirata ranta na ɓaci.


Hawaye saura kiris ya zuba mata, dama bata dawo ba da wannan damuwar da ta dawo ta riska kuma.

"Naji jadda zan gyara yanzu kullum da safe kan in tafi makaranta zan je in gaishe shi ba shikenan ba? Kin turani ɗakin wanchan ya wulakanta ni kin huta!"


Tana kai nan ta tashi ta wuce fuuuu, girgiza kai Jaddah tayi tana furta

"Allah ya shirya Fauziyya"


Ita kuwa tana shiga ta rufe ɗakin tare da yin wurin pillow ta dauki wayanta ta kira Zubair, shagwabewa tayi tana faɗa mishi abunda Faizan yayi mata.


Lallashinta yayi tayi, dukda duk sun sha mamakin yadda aka yi ya ganta, tace ita bazata kara tafiya wani garin ba kuma amma shi Zubair ya tabbatar mata akwai hanyoyi dayawa da zasu bi ba me ganinta.


Satin Faizan biyu aka sanya bukin su da Fatima nan da wata biyu, sbd har sun fara waec.


A take duk bangarori aka fara shiri, ita dae Fauza kaman bata san ana yi ba harkokinta kawai take, ko da Fa'iza ta zo mata da maganan anko ma kai tsaye tace bazata yi ba, su karata chan daga Amaryar har Angon babu abunda ya Haɗata dasu..


Jadda ce ta bada kuɗin nata, Zubair ne yake shirin zuwa Dukda ta ƙi ya ki, wai yayi missing ɗinta Dukda sukan yi waya, su yi video call duka.


Gabaɗaya ya lalatata da soyayyarsa, a gefe ɗaya babu abunda ya sauya daga abubuwan da take yi sai giyar da bata sake sha ba tun daga ranar da abunnan ya faru.


Babanta kuwa ta kan je kullum ta gaida shi, iyaka abunda ke hadasu kenan, wurin mammi ne take girke girkenta hakan ya sa mammi fahimtar abubuwa dayawa daga gareta, har yau bata manta wayar da suka yi da Faizan ba, hakan yasa lokuta dayawa ta kan ja ta da nasihu kala daban daban wadda ya kan kashe mata jiki amma daga ta bar sashen shikenan.


Faizan ya koma bakin aikinshi inda ya Haɗa Fadila da haɗe haɗen kayan aure, dukda ta ce bazata samu zuwa ba sede zata turo ta jirgi se ya karɓa.


Wasa wasa buki ya ƙarato, Amarya da mahaifiyarta ana ta shiri, mutanen Maiduguri sun cika gidan kai ka ce bukin farko kenan a zuri'ar, ba karamin takura Fauza suka yi ba Dukda ta tsaya kai da fata tace babu me saukar mata a ɗaki bukin munafuka da azzalumi, hakan ko aka yi sbd gudun jarabar ta babu wadda ya sauka a ɗakin nata.


Walima, saukar Qur'ani se reception wadda maza ne kawai zasu yi bayan ɗaurin aure aka shirya kaman yadda ake kowani buki a gidan.


Zaune take kan dressing mirror hannunta riƙe da waya tace 

"ka fa san irin gidan da na fito Zubair, yanzu in bar gidan nan in same ka hotel kana Tunanin babu wadda ze fahimta?"


Yace 

"ni dae ki san yadda zaki yi, Haba sweetheart in taso tun daga Abuja in zo har Adamawa don ke kaɗai abinda zaki saka min da shi kenan? Ganinki ma yayi min wuya?"


Tace

"kayi hakuri! Zan san yadda za'a yi na fito"


Yace 

"ko ke fa, ina Green land"


Tace "Toh"


Tsab ta shirya cikin wando jeans crazy da wani armless shirt, ta gyara gashinta sossai ta feshe jikinta da turaruka kan ta ɗauki karamin jacket ta ɗaura saman Rigan ta zumbula hijab ta fito, duk an shiga sallar isha masallaci ga muryar Faizan na tashi cikin nataatsiyar karatunshin nan haka ta fice babu wadda ya lura.


Napep ta tara tayi Jimeta, kai tsaye ɗakin da ya faɗa mata ta wuce, tayi knock ya zo ya buɗe mata tana shigowa ya rungumeta 

"oh my babe, I really miss you wlh"


Ta zame tana furta

"miss you more"


A kujera ta zauna tana zare hijab ɗin jikinta, shishar da yake sha ya mastar mata dashi gabanta ba tare da yace komai ba.


Ta karɓa ta ɗan zuƙa kan tace 

"Wow the flavor is giving.. Wanne da wanne ka Haɗa?"


Ya mata bayani yana karawa da 

"karki damu ba wai bugarwa yake ba kawai dae zaki jiki fresh out of ko wani irin tunani na damuwa ko kunci"


Tace 

"kaman ka san bana cikin daaɗin rai wai yarinyar nan Fatima tun fa da ta sa na bar sashenmu ban sake mata magana ba haka itama, shine yau na shiga wurin Ammi ina fitowa kawai naji tace min wai ina kwana Fauxa, ashar na lailaya mata kawai na ji rankwashe babu faɗar da Baba Alhj be min ba, harda zata bar mini gidan in jika a ruwa in sha, wlh na tsani abu da munafuki in ba don ta kalli baban ba na tabbatar haka zata goge ni mu wuce juna"


Yace 

"Ki kwantar da hankalinki ina ce jibi ne zata bar miki gidan kowa ya huta?"


Kai ta gyaɗa tace 

"bana fata har abada mu sake haduwa in ta tafi kai daga ita har mijin nata ma"


Tana sha ne take ta wannan masifar, lallaɓata yayi tayi da kalamai, daga karshe se gata jikinshi dukda yadda take nuna mai bata so, haka yayi ta rinjayarta, da gasken gaske shedan ke shirin tasiri wurin, tayi saurin mikewa tace 

"bari na zo na tafi kar a kula bana gida"


Yace 

"mu je dae mu ɗan ci abinci kan ki wuce ko?"


Hijab ta dauka yayi saurin karɓa ya ajiye yace

"me haka? A ganni ni Zubair turaki dake da wannan zumbuleliyar hijabin? Inaaa"


Gashinta ya gyara mata ya riƙe hannunta suka fito, da gaske Fauza na da kyaun fusgan hankalin jama'a, shigar ta kuma ya sa kowa ya kalleta se ya sake kallo, kaman ba ƴar musulma ba.


Restaurant suka shiga, yayi musu order har da su fine whiskey, sun yi nisa a cin abincin kaman daga sama taji wata razananniyar murya ta Furta 


"FAUZIYYA!!!"


DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. 

Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.

Acc no. 0545475847 

Acc name. Fatima Muhammad Gurin 

Bank name. Gt bank

Se ki tura shedar biya ta wannan layin

09039206763.

Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰


Karku sake a baku labari.



               🖤Gureenjoh🖤

No comments