Breaking News

Diddigar Kaya 13


 DƘ


13


Kamar yadda rugugin aradu ke sauÆ™a haka sunan nata ya saukar mata barin ma a sadda idanunta suka gane mata wadda ya ambaci sunan, wani irin razana da tsorata tayi har bata san ta miÆ™e kan kafafunta ba, sake ambatar sunan nata da yayi da irin yadda jikinta ke rawa yasa Zubair mikewa yace 

"wai waye wannan É—in ne?"


Takaici ya hana Faizan cewa komai, wani irin fisga yayi mata da saida ta buge da jikinshi ya janye ta suka yi waje saboda idanu dake kansu, motar shi ya karasa ya buÉ—e ya cillata ciki har Seda ta bugu ta saki kara, be damu ba ya sawa motar key, ya juya ya koma cikin hotel É—in Zubair dake tsaye yana kallansu zafin ran dake kan fuskan Faizan kaÉ—ai ya hanashi fuskantar shi Dukda kasancewar shi shima namijin ne, amma an ce wargi ma wuri yake samu.


Shi kuwa Faizan wurin abokananshi ya nufa dama abunda ya kawo shi hotel É—in kenan, abokananshi da suka zo É—aurin aure duk a hotel É—in ya kama musu masauki shine ya zo ya É—an rage dare yaji kuma if they are comfortable with the suits se idanunshi suka mishi mummunar gani, don mummunar gani zai ce dama ya riga ya É—aura alamar tambaya akan wannan yarinya don fitsararta ma kaÉ—ai ya ishi ta fara bin maza, in ba ta san maza ba babu yadda za'a yi ta bushe idanunta akan kowa har uban da ya kawo ta duniya, amma bata yi a wurin da ya kamata ba don yau kakkanninta zata ci.


Runtse idanunta tayi gam gam, gumi na tsatsafo mata na laifin da ta aikata da kuma na rufe ta a motar da yayi babu iska don be sauke window ba, dunkulewa tayi wuri guda kaman sardine ga kanta dake sarawa na abun maye da ta sha wadda ta sha ne don ya ce mata ba wani bugarwa yake yi ba.


Yau dae ta san me kwatarta a gidansu se Allah, dama an ce kwana 99 na É“arawo kwana 1 na me kaya yau dubun ta ya cika, ta maimaita innalillahi wainna ilahi rajiun ya fi cikin chasbi.


Saida ya shafe mintuna sama da hamsin  kan ya fito lokacin har bata iya jan numfashi me kyau don azabar zafi, wayanta ne ya fara ruri, É—auka tayi tace 


"Zubair ka kasheni! Na shiga uku"


Yace 

"Babe wanene wannan É—in? Ya za'ayi ya barki cikin mota window a dage mota a rufe?"


Se a lokacin zazzafar hawaye ya sauko mata tace 

"yayana ne! Kuma wallahi baya ƙaunata ko na sulen kwabo ba rufamin asiri zai yi ba, kashina ya bushe.."


"Yaya zamu yi kenan babe? Ko na saka hukuma?"


Ta zaro idanunta gabaÉ—aya tace 

"whattt? Ka rufamin asiri ka barni da abunda ka ja mini Zubair... Na shiga uku! Gashinan zuwa."

Tana kai nan ta kashe wayar tare da makalewa a cinyoyinta.


A jikin motar ya tsaya ya fara kiran Baba prof.


Bayan ya É—auka cikin ladabi yace 

"Baba akwai wata gagarumar matsala ce da ta tunkaro rayuwarmu wadda dole ce ta sa zan bayyana muku don idan na rufe ma na ha'inceku"


Baba prof yace 

"Kowani bawa da kalar tashi kaddarar da jarabawar, ruwanmu ne mu karɓa ruwanmu ne kar mu karɓa amma idan muka karɓar mun cika wani sashe ne na imaninmu kaman yadda in muka saɓa ya zama kaman saɓawa ubangiji.... Menene?"


Yace 

"baba ku zauna a parlornka ku jirani don fa idan na faÉ—a a waya ba lallai na gamsar da ku ba."


Kashe wayan kawai baba yayi dama yana zaune da Baba Alhj da Jaddah ne, yana sauke wayar ma se ga mammi ta kawo musu tea kasancewar su akwai kaunar sha'i musamman wadda yaji kayan haÉ—i.


"Kai da waye haka? Allah ya sa dae lafiya"

Jadda tayi tambayar.


Cikin nazarin abunda ze faru yace 

"Faizan ne kuma dae kaman ba lafiya ba" 


Tea ɗin Mammi ta zuzzuba ta miƙawa kowa, suka fara sha suna ɗan tattauna abunda ze iya kasancewa don duk tsumayin abunda Faizan ke tafe dashi suke.


Parking motar da aka yi dab kofar baba prof ɗin shi ya sa duk suka maida hankali kan kofar gabansu na faɗi, kaman an cillo kayan wanki haka ya watso ta ta faɗi a ƙasa gashinta ya rufe mata fuska, duk tsaye suka miƙe suna kallonta.


"Faizan menene hakan? Wacece wannan É—in"


Runtse idanu baba Alhj yayi ya sake buÉ—ewa jiri na shirin yarda shi yace 

"Fauziyya???"


Duk kallonta suka yi daidai lokacin ta miÆ™e tsaye tare da janye gashinta tace 

"Na'am"


Da gudu Farhan da shigowanshi kenan ya tare Baba Alhj dake shirin faÉ—uwa amma ya fusge yayi kanta, ya fara dukanta yana cewa 

"ni kike amsawa idanu a sama don tsaurin ido? Fauziyya kasheni kike son yi ki huta? A ina ya samo ki? Kalar tarbiyar shigar da muka koya miki kenan? Innalillahi wainna ilahi rajiun..!!"


Misalta irin tashin hankalin da suka shiga a sannan É“ata lokaci ne, barin ma da suka fahimci a buge take, sossai jadda ke kuka abunda ya kara É—aga hankulansu kenan.


Baba prof ne ya hana a taÉ“a lafiyanta, yace 

"Aisha kamata ku je wurinki, karki bari kowa ya fahimci halin da take ciki zamu yi zama in an watse bukin nan, amma ko kofar parlor ban yarda ta taka ba"


Da kallon takaici da kyama kawai yake bin ta har Mammi ta cire hijab É—inta ta rufe ta don se layi take yi a haka kuma duk wadda ya ganta se a ajiye alamar tambaya, ita kuma ta yafa mayafin kayan ta da ta É—aura a kai ta rungumeta suka wuce cikin gida. Allah kaÉ—ai ya san irin mazan da ta bi da irin surartan nan, haka dae babu daaÉ—in rai aka kira likita ya zo ya duba Baba Alhj da jikinshi ke neman yin tsanani ana gwadawa kuwa jininshi yayi mugun hawa.


Jadda ma jininta se da ya hau bata taɓa zato ko tsammanin hakan daga Fauza ba, yarinyar karama waye yayi influencing nata haka?


Rai babu daaÉ—i aka watse haka bukin auren ya rage armashi don abunda ya tunkaro su in basu yi da gaske ba akwai babbar matsala.


Haka mammi ta saka ta a gaba bayan ta kwantar da ita tana kallo hawaye na zuba mata, wani irin tausayin rayuwar yarinyar na rufe ta, me ta nema ta rasa? Menene ya tura ta ga wannan halaka haka daga gidan mutunci? Mammi ta hana kowa kusantar É—akinta yayinda Ko motsi Fauxa bata yi ba se washegari da rana ya gama fita, amai da ciwon kai ya tasheta.


Mammi na zaune kan sallaya ta idar da wahala lokacin sha É—aya taga tashinta da gudu zuwa bayi, da kallo ta bita har ta É“ace, yadda ta kwana bacci haka duka ahalinta suka kwana kan sallaya suna mata Adu'ar shiriya.


Ko da ta fito zata sake komawa ta kwanta mammi tace 

"Fauziyya"

Ta amsa ba tare da ta iya É—aga idanu ta kalleta ba.


"Koma ki watsa ruwan zafi"

Komawa tayi bayin, bata da wani tunani kuma da zata yi tunda abunda ya faru ya riga ya faru, kafin ta fuskance su ne take jin tsananin tsoro amma yanzu da bayan Kowa ya sani kunya ne ke É—awainiya da ita.


Mammi da kanta ta aika aka É—auko mata kaya, ta sa aka hada mata abinci aka kawo har É—akin, sadda ta fito ta shirya mammi ta mata nuni da tray É—in, haka ta janyo ta ci sbd yunwa dake dawainiya da ita, rama sallolin kanta tayi duk abubuwan nan bata yarda ta HaÉ—a idanu da mammi ba sbd kunya.


Bayan ta idar ta gaida mammi tana wasa da kasan hijab É—in nata.


Mammi ta amsa kan tace 

"Fauziyya"


"Na'am mammi"


"Fauziyya kin san irin rayuwar da kika jefa kanki kuwa?"


Kanta na Æ™asa hawaye ya fara kwarara bisa fuskanta tace 

"mammi Adu'a Zaku yi min, nima ban san me yake damuna ko meyasa nake fadawa halaka bayan na sani ba, wani lokacin kasa fahimtar kaina da rayuwa ta nake, chan kasan zuciyata bana jin daaɗin hanyar da na hau sai de wani zuciyar na tirsasani ƙarbar hakan ta wani fuska..."

Kuka ne ya ci karfinta.


Mammi ma hawayenta na tsananin tausayin Fauzan ta share, tace 

"É—auko Alqur'ani ki karanta Fauziyya"


Mikewa tayi tayi yadda mammi tace, tayi karatu har azahar suka yi salla tare, kan mammi ta sa ta sake kwanciya.


An yi walimar Fatima Dukda sun fahimci armashin auren ya ragu sossai sai de babu wadda ya san dalili washegari aka É—aura aure aka yi saukar Qur'ani.


Ko kofar É—aki kaman yadda Baba prof yayi umarni Fauza bata taka ba, ta ci abinci tayi ibada se tayi bacci, duk tunani ya fara cin karfinta ita yanzu ko wayanta bata san hannun da yake ba, taji mammi na maganar Amarya zasu kai wani sati kan su tare don haka daga washegarin É—aurin auren mutane dayawa suka watse.


A daren Ammi ta zo ta sashen mammi daga bakin kofa ta tsaya tace 

"ke Fauziyya! Tunda ba a nan aka binne cibiyarki ba ki tashi ki wuce mu tafi, tun aka fara hidimar nan neman duniya na yi miki babu wadda ya iya buÉ—e baki ya ce min ga inda kike? Meyasa ne ake nema se an tauye min hakkina a matsayinki na Æ´ata kaman yadda aka tauye min sauran hakkokin nawa? Me kuma aka ce kinyi wannan karo?"


Kanta ta É—ago tace 

"Ammi kiyi hakuri"

Ammi ta aika mata da wani kallo tace 

"ban gane ba? Kinga tashi mu tafi mayi maganar kaman kowacce uwa da Æ´a a É—aki"


Mammi tace 

"baba prof yayi umarni akan ko kofa be amince ta taka ba har se ya neme ta"


Wani irin kallo Ammi ke mata 

"wani ta kashe ko mene?"


"Wannan kuma shi zaki tambaya Ammin su"


Neman tada zaune tsaye take wai baba Alhj ya ki ce mata komai, Jaddah ta ƙi ce mata komai sannan yanzu zata zauna da yarinyar ta ace ba haka ba? Akwai wadda ya haifa mata ne..


Baba prof be so hankalin kowa ya dawo kan abun ba amma saida Ammi ta janyo hakan Dukda yadda Fauza ke hanata maganan.


A take kowa ya san akwai abu a ƙasa, hakan tasa ya kira meeting kawai.


Kowa da kowa har da Amarya ta hallara, babu wani bare duk mutanen gidan ne.


Kai tsaye ya buɗe taro da Adu'a kan ya fara magana akan jarabawar yana misalai da magabata akan dole Allah ze jarrabeka ta hanyar 'ya'yayenka wani dukiya wani mata babu yadda babu kaman yadda mahaifin Annabi Yusuf annabi yaqub yake annabi amma 'ya'yanshi suka so halaka ɗan uwansu, kaman yadda annabi nuhu yake annabin Allah amma ɗan shi ya fita yana saɓawa Allah har Allah ya halaka shi tare da sauran masu saɓo, misalai dae kala kala.


Daga karshe ya É—aura da 

"Ina so duka mu É—auki Fauziyya as zakka, ba kuma wai zamu sakata a gaba da hantara da kyara da kuma duka bane, babu wadda ze É—aura hannu a kanta da sunan duka idan har ka cika cikakken masoyinta da halakarta ka iya jefaka cikin alhini to ka tsaya mata akan sallaya ka rage mata bacci musamman iyayenta"


"Menene Fauziyyar tayi?"

Ammi ta jefa tambayar don ita duk waennan wa'azuzzuka sun ishe ta.


Baba prof yace 

"mun zauna da Faizan ya faɗa min ganin da yayi mata a wani hotel a Abuja wadda kai tsaye ya faɗawa mahaifiyarshi ita kuma ta ƙi aminta sbd sanin da sa hannun makaranta aka tura Fauziyyar excursion Gombe, wannan kaɗai alamar tambaya ne don haka muka yi tattaki zuwa makarantar Allah ya sa abokina wadda shine mai makarantar ya zo musamman daga Maiduguri ɗaurin auren Faizan, anan muka tabbatar da manuplating malamin Fauziyya tayi yayi musu takardar bogi suka tafi Abuja saide be san me ya kaisu ba"


Babanta yayi salati ya sallamar yace 

"yanzu Fauziyya a iya shekarun kin nan har kin san kiyi manuplating malami ya barki ki tafe watsewa uwa duniya? Bazaki kasheni ba Fauziyya..."


Baba prof yace 

"Sulaiman karka manta duk abubuwan da nace kan mu fara tattaunawan nan, malamin karan kanshi na da laifi don da be yi abunda zata yi manuplating nashin ba da bata yi ba, shima nemanta ya so yi tayi recording ta juyar kanshi ga wayan da bamu san tana da shi ba hannun Faizan komai na ciki don a motar shi ta bari"


Da sauri ta É—ago ta kalleshi shi kam ba ta ita yake ba, kawai yana zaune ne don ya san abun ya shafe masoyanshi da kuma gidansu amma da don ta shine wallahi ko a jikinshi, sarai ya san Zubair drug dealer ne wadda EFFC da NDLEA sun sha kama shi su sake saboda É—aurin gindin da yake dashi, ya shata mishi katoton layi ya kuma gargadeshi a wayan na Fauza da yake ta  kira akan in har yana cin Æ™asa to ya kiyayi na shuri.


"Fauziyya me ya kaiki Abuja?"

Jadda ce tayi maganan har muryarta na rawa.


Shiru tayi kanta ƙasa, wani tsawa da babanta ya daka mata yasa ta ɗago kowa idanunshi na kanta se ta nemi rikicewa..


"Mun je birthday party ne"

Duka parlorn salati ya É—auka, ga É—iyar gidan baba prof a birthday party har Abuja.


"Ke da waye"

Baba ya jefa mata tambayar 

"ni da sakina da rahama, wlh baba duk partyn da nake zuwa a cikin garin nan ne wannan shine karo na farko da muka tafi Abuja"


Salati aka sake dauka yarinyar kaman aljanu ke displaying É—inta don ita fa idan lokacin abu yayi a yi shi, gaskiya komai dacinta fede ta take idan har ya kama É—in.


"Unbelievable! So you have been doing this for long?"

Faizan ne ya jefa mata wannan tambayar.


Shiru tayi.

Ya sake cewa 

"wayan dubu É—ari uku a ina kika samu?"


Tace 

"wan...wani ne ya sa...ya min"


Farhan da su Faraj ji suke da a basu ita su yagalgalata ko zata yi bayani da kyau amma baba prof ya hana.


Ido kaman ze cinyeta tace 

"baba wlh ni ban yi niyyar shan giya ba, Zubair ne ya munafunceni ya saka min cikin coke, shekaranjiya ma shisha ce kuma ce min yayi flavor ne ciki baya bugarwa shiyasa na sha"


Rasa me magana aka yi a parlorn Amminta ne ta rufe ta da duka tana kuka tana cewa duk wani abunda ze sa ta tozarta ta idanun kishiyoyi tayi, gashi har wasu na jin daaÉ—i nasu shiryayyu ne ita kuma gurbatacciya, ita kam bata koya mata hakan ba sai de in a wuraren da take zama aka hore ta da hakan.


Mammi ce ta kwace ta sauran matan parlorn duk babu wadda ya motsa, bakinta har yana jini ta lafe jikin mammi tayi shiru.


Nasiha me tsayawa a rai Baba prof yayi musu, ya kafa mata sharaɗoɗi babu ita ba sakina da rahama, babu ita ba boko ze biya mata neco tunda an yi nisa da waec tayi shima lokacin in yayi da sa ido sossai zata yi, ko bakin gate aka sake ganinta da kanshi ze ɗauki mataki a kanta, manyan be yarda kowa ya sake dawo da abunda ya wuce ba suyi ta mata Adu'a, sadaka da saukar Alqur'ani, yaran kuma in sun yi ma sun Santa don haka kar a kawo mishi ƙarar ta in aka goge ta da magana ta rama.


Rayuka dayawa ba haka suka so abun ya tsaya ba, sai de ya suka iya, haka ta koma sashen jadda da ta zage tayi ta mata nasihu batayi fushi da ita kaman babanta ba.


Bayan sati É—aya Faizan ya É—auki matarshi suka koma Abuja dama an je an mata jere, ita kam Fauza ta zama kifin gwangwani hakan ya dawo da halin ta na da kannenta basu isa sun sake a gefenta ba, haka duk wani wadda ya gayamata magana akan rayuwarta se ta gayamai shuwaka, ana haka sakina ta shirya ta zo gidan...




DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuÉ—i ne.. 

Ze zo muku a Naira É—ari uku kachal #N300.

Acc no. 0545475847 

Acc name. Fatima Muhammad Gurin 

Bank name. Gt bank

Se ki tura shedar biya ta wannan layin

09039206763.

Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰


Karku sake a baku labari.



               ðŸ–¤Gureenjoh🖤

No comments