Breaking News

Diddigar Kaya 14


 DƘ


14


Daga bakin gate ta tambayi sashen Jaddah tunda ba zuwa gidan suka taɓa yi ba, mai gadi kuwa ganinta da jumbuleliyar hijab ya zata irin baƙin da jadda kan yi ne don ba'a raba ta da jama'a daga sashenta har sashen mammi, da hannu ya nuna mata sashen ya dae tabbatar mata jadda bata nan sun fita barka da sauran matan baba prof karshen layi.


"Babu komai zan bada saƙo ne kawai in juyo"

Da sauri tayi sashen tana shiga parlor ta fara kwala kiran Fauxa, da gudu ta fito jin muryar da ta sani ne tana ganin sakina kuwa ta rungumeta da murna.


"Kina lafiya Fauxa? Ai hankalinmu duka a tashe Zubair ya ƙi tafiya Sam wai se ya tabbatar da babu abunda aka miki a gida, yanzu haka ma shi ya kawo ni yana farkon layin nan"


Jan ta Fauxa tayi É—aki tace 

"babu abunda aka min sakina sai de na zama matar ƙulle, kowa baya sake min fuska musamman waenda muka yi sabo dasu, har baba prof gaisuwa ta kawai yake amsawa, ke a takaice dae gabaɗaya duniyar baya min daaɗi, ba cireni school bane damuwa don makaranta be dame ni ba amma rashin fitan nan ga aiki don yanzu dole in ke komawa sashen mu ina aiki tunda babu wani aiki sashen jadda, komai fa ni nake yi tare da umarnin Baba Alhj"


Sakina tace 

"kaiii wannan rayuwa na gidan nan Allah dae ya fidda ki, yanzu ko gate baki leƙa wa?"

Na kara tabbatar mata da ko gate ba'a yarda in leƙa ba idon yayyuna duk a kaina yake, yanzu an yi min registern neco tunda an riga an gama waec ina ga shine kaɗai abunda ze sa na taka waje.


Wayar ta karamar touch ta mika mata tace 

"gashi ki riƙe a hannunki zamu yi magana, bari naje tunda kin ce ko mu an rabaki damu wayanki kuma mugun wan ki yayi miki ajalinshi"


Karɓa tayi tana mata godiya harda jajjada mata bata san irin taimakon da tayi mata ba don bata san tana son Zubair ba seda aka katangeta da sauraron muryarshi.


Bata raka sakina ba don kar a gane, amma a fita saida sakina ta hadu da Fa'iza da kallo kawai fa'iza ta bita har ta fice, fasa shiga gidansu tayi tayo wurin Jaddah.


ÆŠakin Fauza ta tura da sauri Fauza ta boye wayan karkashin pillow.


"Malama ya da shigo min É—aki babu sallama?"


"Fauza me Sakina ta zo yi a gidan nan bayan irin kashedin da aka yi miki?"


Wani irin kallo Fauxa ta watsa mata 

"last da na bincika dae sunanki ba ruqayya ba! Uwata kenan ko? Sannan a shekaru kin san na girmeki don haka ki fita sabgata kaman yadda kike tun farkon fara sabon rayuwata babu ruwanki, in kuma kika ƙi kin san halina bani da kyau ko na sulen kobo wallahi"


Idanu kawai fa'iza ta zuba mata kan ta girgiza kai tace 

"Allah ya shirya"


A masifance Fauza tace 

"Ameen in da gaske kike, kema na lura yayarki kan ta tafi ta tsammiki wannan munafurci nata in ba haka ba yaushe kika yi wani buÉ—ewar idon gayamin magana yen yen yen da fuska kaman nawa anan"

Har Fa'iza ta bar parlorn tana jin masifar Fauxa.


Ita kuwa fa'iza na kulewa ta fiddo wayan dake ringing, Zubair ne nan ta gayamashi duk abunda aka yi mata a gida

"yanzu wani mataki kike shirin É—auka?"


Tace 

"ka bari tukuna in ga matakin su don na tabbatar ba shikenan ba, shurun  baba prof wani abun ze kulla wadda babu wadda ze yi zato ko tunani, amma in na fara fita necon zan san yadda zan yi muke haduwa for now mu dinga wayan kawai"


Haka ta kasancewa Fauxa, kullum in ta tashi asuba bazata dawo sashen jadda ba se ta gama komai na sashensu ta kan yi mamakin Amminta wacce bata rabo da maganan Fauxa kin wulakantani kin zubar da ƙima ta a idanun kishiyoyi, hakan yasa har ta gama ayyukan idan ba gaisuwa ba daga babanta, mamanta har Aunty Amarya babu wadda take sake tankawa.


In ta gama na sashen ta koma sashen jadda tayi na nan da aka ware mata, kan ta karya, jadda zata sakata wucewa ta gaida duk matan gidan, bata fitowa daga sashen mammi kuwa se da nasiha me tsayawa a rai, hakan be hana ta waya da Zubair ba, sossai yake kara riritata yana hure mata kunne akan rayuwar gidansu ba rayuwa bace takura ce.


Ana haka take samun labarin É“arin da Fatima tayi, dukda babu wadda yake magana akan zaman su don haka bata san yadda suke yin ta ba amma ta tabbatar kowa se da ya shiga damuwa kan wannan bari har Fa'iza aka tura dake an gama jarabawar makaranta Hutu ne kawai za'a bada abunda ba É—abi'ar Baba prof ba, don baya yarda wata cikin en matanshi taje gidan wata zama da ko wanni nufi kuwa.


Ko a jikin Fauza kaman ma bata san me ake yi ba, bayan sati biyu da tafiyar fa'iza ta fara Neco, driver musamman aka ajiye mata shi ze kaita ya jira har ta fito ya dawo da ita, to ranan baba prof ya fita za shi unguwa da ya Faraj kenan ya hangi wata yarinya me irin uniform É—in Fauzan a farkon layi saka Faraj parking yayi ya kira mishi ita.


Ko da ta zo ya tambayi sunanta se ya gane mahaifinta mutum ne da baya ƙaunar shi don ko sallah baya zuwa masallacin shi ta bayan layi yake zuwa, murmushi kawai yayi ai ya riga ya san ba kowa ne ze so ka a duniya ba amma tunda akwai hakkin makotaka ze sauke.


"Zan sanya driver da ke kai Fauziyya ya dinga biyowa yana daukar ki se kuke tafiya tare kuna dawowa tare se ya fi miki sauƙin neman abin hawa a nan wadda suke wahala"


Har ƙasa ta duƙa ta mishi godiya Dukda kwarjini ne kawai da ya cika ta dashi in ba haka ba babu abunda babansu be faɗa musu akan Prof kaka ba.


Haka ko aka fara, abunda ya fara ba Fauxa haushi yadda yarinyar take shigowa har su je su yi paper su dawo bata gaisheta, dukda ita ba kalar wacce ta damu da damuwar wasu bane sede haushi ya kan cika ta da al'amarin yarinyar kina cin arzikin mutanen gida kina musu gadara.


Wata rana suna da papern rana tun da suka fito ma Fauxa ke wayanta da Zubair don yau din zasu haÉ—u a makarantar, musamman ya kawo wadda ze zauna yayi mata papern ranar a madadin ta ita kuma su fita tare.


Ko da ta isa bata nufi hall ɗin ba ta zagaye bayan classes anan Zubair ya ɗauke ta suka fita, ya nuna mata yayi kewanta ta amince mishi sau ɗaya dae kan ta gama paper ta koma kulle, lallaɓa shi tayi akan tunda suna son juna ya turo magabatanshi in ya so tana gamawa baban ya ɗaura mata aure su huta, yace ze yi tunani akai haka dae suka gama yawon su ya haɗo ta da chocolates masu yawa.


Ko da ta dawo kowa ya waste a school wanchan yarinyar se tsaki take ja, driver dae sanin halin Fauza yau ne kuma na biyu na farko sun hadu har dasu sakina yasa be ce komai ba.


Koda ta zo bata ce musu su yi haÆ™urin ajiye su da tayi ba kawai ta shiga ta zauna abunta tana bare diary milk, har sun kusa unguwarsu yarinyar da ko sunanta bata sani ba tace 

"Fauziyya sunanki ko? Nace ya kamata kike sanin darajar mutane, don ana cin arzikin gidanku ba shi ze sa ki samu damar wulakanta mutane ba, sannan wallahi kika yi tsiya se in yi tattaki har gaban tsohon ki in sheda mishi abunda kike yi in kin fita, ko de!"


Ta taÉ“e baki tace 

"na ji labarin da saninsu ma tunda arzikin na safarar yara ne ko me nasu tayi sakamako n....."


Wani kalar buge mata baki da hanci da fauxa tayi da gwuiwar hannu se da yasa hancin ta da bakinta fara zubar da jini.


"Da alama baki san Fauxa bane! Ina me tabbatar miki wannan gargadi ne É—on wannan ne karo na farko ko da bakin wasa wannan kazamtacciyar bakin naki ya sake ambatar iyayena ko da Kalmar alheri ne se na gurje shi bare ta tsiya"

Tana gama faÉ—a ta saka hijab yarinyar da already ya É“aci da jini se yarfa hannu take tana kuka ta share bayan hannunta, don kowa ya san Fauxa er gayu da kwalliya ce, kayan ta bata yarda wani stain ya bata su.


Driver ne yace 

"ashhha! Hajiya Fauxa ayi haƙuri ai duniya ɗan hakuri ne"


Bata ce mishi komai ba sbd be saba shigar mata idanu ba wannan ne na farko kuma ta É—aga mai kafa, yana tsayuwa yarinyar ta sauka da gudu tana kuka ta shige gidansu.


Tsaki me karfi fauza ta ja tana rasa me ke damun baba prof da manna waenda basa kaunarka jiki.


Ta samu fa'iza ta dawo da sha tara na arziki don sayayya me dumbin yawa Faizan yayi mata matsayin kanwarshi, kowa seda ya samu tsarabar shi kasancewar shi mutum me kyauta sossai.


Washegari ko da suka tsayawa yarinyar bata fito ba Fauza tace su wuce, a makaranta ta samu yarinyar da wasu mates É—inta don ita bata san makarantar ba tunda jarrabawa ne kawai ya kawo ta sbd gudun haduwa da su sakina yasa baba yayi mata registeration a wani makarantar.


Yadda suke ta hura hanci ga yarinyar fuska a kumbura yasa Fauxa kwashewa da dariya, irin kallon da suke mata na zaki daku yau tayi musu kan tayi wucewarta, bayan sun gama paper an waste tana tahowa don zuwa wurin mota en matan huɗu suka yi mata ƙawanya.


"Ke! Me kike takama dashi da zaki illatar da sukaina kuma kiyi Tunanin kin ci bulus?"


Sha ka hura dake bakinta ta ciro ta É—an lasa tana Kallonsu dariya suke bata.


ÆŠayan tace 

"don an zagi prof kaka menene? Waye be san yadda kudinshin nan dake ta hauhawa ba na Allah da annabi bane? Ko karya aka yi don an ce yana safarar mata?"


Dayar tace 

"ai ba mata da yara kaɗai ba har abubuwan shaye shaye don duk abunda kaji ana jita jita a kai da ƙamshin gaskiya"


Na farkon tace 

"karki kai da nisa gashi har yaran yake baiwa suke sha, waye be san wannan Æ´ar fitsitsiyar babu abunda bata sha ba?"


Jakarta Fauxa ta sauke ta buÉ—e ta ciro paper ta fara naÉ—e sha ka hurarta na big bom, tana nadewa ta fara magana.


"Kaman yadda na miki alkawari bakinki ya sake aibata iyayena se na gurje shi to yau se na gurje shi da ƙasa idan gasa miki shi ne ba'a yi da kyau ba yayin wankan haihuwa yau za'a miki gashi me kyau..."


Tana kallon sauran tace 

"ku kuma en korenta kowaccenku sakamakonta na rubuce a goshinta, ke yatsar da kika nuna ni dashi yau se an yi miki gyara, ke kuma haƙorin ki ɗaya se kin rasa shi, ke kuma zaki komawa uwaki da karyayyen hanci kin san Karyewan cartilage? To yau zaki sani"


Tana kai nan ta cire hijab ɗinta ta ninke, da gudu tayi cikinsu suka fara dambatuwa, dukda kwana biyu rabon da tayi faɗa tana acting classy yau seda ta zage tayi musu duk abunda tace don bata taɓa faɗan magana ta kauce akai ba.


Tana yi tana cewa 

"Da kun tambaya tun farko waye Fauxa da baku shiga sabgata ba"


Duk saida ta cika alkawarinta kan da kyar aka dagata kan su.


Taje ta É—auki hijab É—inta tana haki ta saka ta É—auki sweet É—inta ta cigaba da tsotso tare da rataya jakanta tayi mota, ko da suka dawo gida ita har ta mance ma da abunda tayin.


Chan dare tana cin Samosar da tayi bayan dawowarta da tea kawai Ya Farhan yayi sallama 

"Fauziyya zo mana"


Dukda be saba mata irin kiran ba haka dae ta miÆ™e ta bishi É—akin su taga yayi, a zuciyarta take masifan Allah ya sa ba aiki ze saka ta ba, tana sanya kafafunta a É—akin ya maida kofan ya rufe, Faraj dake zaune da dorina yace 

"na lura barin ki da ake shi ya sa ko yaushe kika tashi ɗauko mana magana se ki ɗauko kalar wadda ba'a taɓa yi ba, bana Tunanin ko hanyar police station baba ya sani amma wai yau a ta sanadiyarki aka zo har wurin karantarwar shi za'a daukeshi.."


Takaici ya hana farzan din cigaba da magana, Farhan yace

"Fauziyya yau zan tabbatar da na huce duk takaicin da nake kwasa akanki, yau ɗaya zan saɓawa umarnin Baba na be amince kowa ya taɓa ki ba in yi miki dukan sauke takaici, wawuya wacce bata san me ke mata ciwo ba.."


Dukda yadda zuciyarta yake bugawa, bata nuna a fuska ba, ta san sun fi karfinta kuma ihun duniya tayi anan babu me jiyo ta bare a zo cetonta gwara ta sallamar kawai su kashe ta in sun so.


"In de akan yaran da na daka ne wallahi ko gobe suka sake maimaita abunda suka yi haka zan musu, ba police ba su kawo rundunar sojoji...."


Bulalar da Farhan ya fara sauke mata cikin takaici ne ya katse mata maganar, dukan kawo wuƙa suka mata tun tana ihu har ta dena tana jiran kawai su kashe ta, har hijab ɗinta seda bulala ya yayyaga fatanta har jini yake yi..


"Tashi ki fice ko in kasheki kowa ya huta"

Farhan yayi mata ihu hawaye na zuba a idanunshi, iyayenshi yake ji wa takaici, be taɓa ganin baba prof a yanayin da ya ganshi yau ba, wai har wannan yarinya ta ja ake gayamishi maganan da ya saka shi zub da hawaye dukda be yarda kowa ya gani ba amma sun san ba karamin zafi ya mishi ba.


Da sauri ta fito tana layi, dishi dishi take ganin mammi tsaye tana kwala kiran sunanta, Sam bata san ma da wani a gefen mammin ba ta de ji tana cewa 

"kama min ita... Yi sauri kama min ita, innalillahi me zan gani haka?"


Yanke jiki tayi sbd yadda duk garkuwar jikinta suka karaya suka gaza É—aukar gangar jikinta a hannun mutum ta ji ta kan ta karasa ficewa hayyacinta.


DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuÉ—i ne.. 

Ze zo muku a Naira É—ari uku kachal #N300.

Acc no. 0545475847 

Acc name. Fatima Muhammad Gurin 

Bank name. Gt bank

Se ki tura shedar biya ta wannan layin

09039206763.

Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰


Karku sake a baku labari.



               ðŸ–¤Gureenjoh🖤

No comments