Breaking News

Diddigar Kaya 3


 DIDDIGAR ƘAYA 

   (Mai Wuyar Tsincewa)


بسم لله الرحمن الرحيم 


FATIMA MUHAMMAD GURIN.             

         (Gureenjo)


ADABI WRITERS ASSOCIATION 


Marubuciyar:

*Zuhraa*

*Hamrah*

*Igiyar Rayuwa*

*Noor Iman*

*Ruwan Sama..*

*Lelewal*

*GAMON JINI paid*

*Kowa Ya ga zabuwa..*

And Now..

*Diddigar ƙaya... Paid*


                      *Shafi Na Uku*


*PAID BOOK*


ƊANƊANO


**WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI MRSJMOON GWANATA KUMA SHUGABATA🥰❤️**


*SOME YEARS BACK*


"Fauxa! Fauxa!!"


Muryar ke fitowa daga tsakar wawakeken gidan yana amsa kuwwa a duk saƙo da saƙo na cikin gidan, har matsakaiciyar matar ta iso kofan ɗakin tare da yaye labulen sbd kofar dake wangale bata fasa kiran sunan ba.


Turus! ta ja ta tsaya tare da wara ido Kalmar 


"kan uban chan!" Ya fito daga matsakaitan laɓɓanta.


"Fauziyya! Ashe sunanki daaɗi yake min da zan kama in yi ta kira kina ji ki min banza? Ni sa'ar ki ce? Ko kin maida ni irin su fa'iza ne?"


Kyakyawar matashiya ce me ɗauke da coffee colour skin, irin skin ɗin nan da ake kira glass skin da ake wa magana na zaune saman bed me yanayi da gadaje irin na hostel hannunta chocolate ne na bounty tana sha, a hankali ta ɗago manyan idanunta  da kwayar suke kalar Grey ta watsawa matar tare da motsa kyawawan siraran lips ɗinta wadda ya saka cikakken girarta me cike da gashi suka haɗe wuri guda cikin kunkuni tace 


"Ai an san inda mutum yake ba se a zo a same shi ba, sai an yi ta mishi kiran kasuwa!"


Ta karasa da murguɗa baki.


Wara idanu matar tayi tace 

"Me kike cewa?"


Da karfi tace 

"ni ban ce komai ba, gani..!"


Tayi maganan tana dirkowa ba tare da ta bi matakalar da aka tanada don hakan ba ta je gaban matar ta tsaya kerere, tsiririya ce me kananun shekaru bata da kauri da matukar wuya ta haura 16yrs karamin shape da take dashi ya haɗu da tsawon ta ya bata wani kyaun sura na musamman, manyan idanunta da dogon hancinta zuwa lips ɗin ta sun taimaka wurin fitar da ainihin kyaun da Allah yayi mata musamman in ka Haɗa da yanayin skin color ɗinta.


"Ki wuce ki je ki yi min wanke wanke tunda zuwa Islamiyya ya gagareki, Fatima bata samu tayi ba sbd lokacin islamiyya da ya shiga"


Baki ta turo tace 

"ni ba zan yi wanke wanken da ba na rana na ba fa! Me anfanin rabawar to in an san za'a zalunci mutum? Ni de! Ni de......"


Ɓassss haka karar Marin da aka yiwa bakinta ya bada sauti da sauri ta ɗago don ganin waye ne ta sauke mishi tijarar ta da be bar kan kowa ba, se suka Haɗa idanu da Ya Farhan zaro mata idanunsu iri ɗaya yayi yace 

"fitsararriya ana magana kina yi, ki wuce ki je maza ki kama wanke wanken nan tun ban sauya miki kamanni ba.."


Baki ta zumburu tana kunkuni

"mugu, azzalumi..!"


"Me kika ce?"


Tace 

"cewa nayi to bari na fito"


Ta Raɓa ta wuce tana ci gaba da kunkuni musamman da taji Aunty Amarya na cewa 

"da baka kai mata hannu ba ai Farhan, yaran ne se Adu'a yanzu"


"Munafuka, guntuwa..!"


Ta faɗa bayan ta sauka tana bin kan interlocks da suka zagaye sashen wadda har daga wajen karamar kofar da nake hange a buɗe su ke zube.


Tsakar gidan an yi kaman roundabout na interlocks inda tsakiyar kyakyawar bishiyar Almond wacce aka fi sani da umberalla ta kawata gidan, chan gefen kitchen da store ɗinsu aka yi wurin wanke wanken dake lailaye da tile, Fatima ta riga ta gama Haɗa wanke wanken har ruwa da komai, farawa tayi tana me cin alwashin wlh ranar wanke wankenta baza tayi ba sede Fatiman tayi.


Tana wanke wanken tana ta bubbuga kwanuka har Seda Ammi ta leƙo tace 

"ke kam lafiyanki kuwa?"


Kallon farar matar tayi wacce suke ɗan yanayi ta tsawo da hanci tace 

"ƙalau Ammi"


Girgiza kai tayi ta koma tana sauke labulen ta duk ta ji abunda suka yi da Amarya, bata mamakin halayen Fauxa don kowa ya kwana ya tashi ya san wacece Fauxa a gidan, zama tayi cikin kujerun parlorn nata tana ta tufka da warwara wadda bata rabo da shi a kullu yaumin na kwanan duniya.


Har Fauxa ta gama wanke wanken ƴan islamiyya basu dawo ba, hijab ɗinta ta janyo daga saman igiya dake ɗaure a tsakar gidan ta saka tana me ficewa kar wannan guntuwar Amaryar ta Haɗa ta da aiki.


Masha Allah, tsakar gida ne me matukar yalwa, shimfiɗe da interlock ƙawace da flowers kama daga koraye, jajaye, ruwan ɗoruwa da kuma farare chan gefe parking space ne, se parts babba guda ɗaya, wadda nasu ne na biyun girma se wani ƙarami a gefe, da kuma wadda be kaishi ba daga gefe. daga cikin gidan wani babban masallaci ne da yafi gidan ƙawatuwa, babban kofan ta waje ne sede akwai wasu kofofin kama daga na maza har mata ta ciki.


Karamin part ɗin tayi tana shiga ta fara ambatan

"Jaddah! Jaddah!!"


"Maza to cire min dodon kunne Fauziyya se ki huta"


Baki ta chuno wadda kaman ɗabi'ar ta ne na lura, tana shiga parlorn matar bayan ta cire takalman ta daga bakin varendern tiles dake shimfiɗe daga kasan kofan.


Parlor ne madaidaici sede ya wadatu kwarai da kayan more rayuwa, cikin ɗaya daga cikin kujerun ta kalli dattijuwar wacce kamanninsu har ya ɓaci da yarinyar tace 

"Haba jaddaty ai ni dake Bama ƴar haka"


Jaddah na jin haka ta san wani jarabar Fauxa ta kwaso, tace 

"Toh ina ji yanzu kuma me ke tafe dake?"


Fauza na zama daga kasa ta kama mammatsa kafafun tsohuwar tace 

"Ban je islamiyya da karatu ba kuma kin san anjima se Baba Prof ya aiko kirana"


Ta faɗa a marairaice 

"in ba'a yi sa'a ba se ya sa su Faisal zazzane ki"

Jaddah ta karasa mata.


Raurau tayi da idanu ga tsoro ga neman rigima, babu abunda take tsoro irin bulala kuma tana dakuwa kam sbd rashin jinta da neman rigimar ta babban shine rashin kunya.


"Ki taimakeni jadda kar baba prof ya san lafiya ta ƙalau ƙin zuwa nayi, wlh na gaji ne kullum kullum abu ɗaya bawa baka da hutu ko kaɗan"


Sallama aka fara daga ɗan harabar na jadda wadda ya sakata saurin cewa 

Fauza 

"yi maza hau kujera ki kwanta ki kuma rufe fuskanki da hijabi, maza maza"


Da gudu kuwa ta haye tare da janye hijabinta ta rufe fuskan nata.


"Wa'alaikumussalam waye ne kaman Farhuddeen?"


Saurayin ya karaso yana sanye da blue riga da wando me taushi tare da hular taɓani kaji hadisi yace 

"nine Jaddah dama baba prof ne ya aikoni in kira masa Fauxa se kuma Aunty Amarya tace min yanzu ta gama wanke wanke baze wuce nan tayo ba"


Jadda tace 

"eyyaa ai kuwa nan ta shigo zazzaɓi ya rufe ta kwab ɗaya dama wanke wanken ma da kyar ta gama shi sbd kawai Amarya ta matsa ne, ka ce mishi bata jin daaɗi"


Ko rantsuwa ze yi baze yi kaffara ba lafiyar Fauxa ƙalau tsabar sonta da jadda ke yi yake sa take goya mata baya lokuta dayawa irin wannan, kwafa yayi yana hararanta kan ya juya ya fice.


Seda ta tabbatar ya fita kan ta wanckalar da hijabin tana saukowa hakwaranta farare Kal da kaman jera su akayi a waje.

"shiyasa nake matukar yinki tawan, shege ya Farhuddeen ina Kallonshi yana harara ta ta wuyan hijab kawai ba yadda ya iya dani ne"


Hira suka cigaba da yi da jadda sbd duk jikokinta kowa ya san mutane biyu ne mafi soyuwa a wurinta se kuma aka samu akasi suka kasance WUTA DA AUDUGA.


Dab magrib suka ɗauro alwala a harabar na Jaddah suka fito don zuwa masallaci, ɗabi'ar gidan dole duk me kake yi kan magrib ka tabbatar ka gama daga mazan har matan a kira sallah kana cikin massallaci ana kira kuna amsawa kaman yadda addini ya koyar daga karshe ayi Adu'ar bayan kiran sallah se a yi sallah, in an idar za'a yi azkar bayan an gama za'a yi nafila kan kowa ya ɗauki Alqur'ani daga ma'ajiyar Qur'anai na massallacin a hau karatu har zuwa lokacin da za'a kira isha a gabatar ayi nafila karfe takwas na dare kowa ze koma gida don cin abinci da sauran hidimdimu haka da asuba kiran farko dole kowa ya mike ya hau shirin massallaci har yaro ba'a bari, ɗabi'a ne da suka tashi suka tarar ana yi wadda basu san iya tsawon lokacin da aka ɗiba ana yi ba.


Tun kan su isa massallacin suka hango ƴan mata wacce zata ɗara Fauxa ɗaya se kuma waenda basu kaita ba su uku se wasu guda biyu da zasu yi sa'anni da ita duk tafiyar daban dabance.


Kau da kai tayi ta cigaba da hiranta da Jaddah, bayan sun shige kowa ya zazzauna chan se ga Aunty Amarya da Ammi sun shigo sanye da hijab, daga bayan su mata ne guda huɗu ras, a kallo daɗɗaya zaka iya faɗin kai tsaye biyu Fulani ne, sbd yanayin haskensu se biyu baƙaƙe waenda kuma suke da zane wato tsaga irin na kanuri.


Duk gaban jadda suka duƙa suka mika gaisuwa, ta amsa da fara'arta kaman kullum, Fauza ta kalli wata babbar mace daga ciki tana da dirin jiki Dukda tsufa da ya fara bayyana mata kuma fara Kal me yawan fara'a wadda be ɓoye hakwara biyu na hajji dake bakinta ba tace 


"Mammi sannu, ya ciwon kafan?"


Da tsantsar kulawa Mammi ta kalleta tace 

"sannu Fauxa, kafa da sauƙi idon ki kenan tun asuba ko?"


Murmushi kawai tayi, ta juya ga sauran matan kaman dole tace 

"maami, umma da dada sannunku"


Ba don idanun Jaddah dake kansu ba babu wacce zata amsa a cikinsu sbd haushin rainin wayaun Fauxa da a kullum kaman kara karuwa yake, gyaran muryar loudspeaker da ya karaɗe ilahirin unguwan da kiran sallah yasa duk kowa ya samu sahu ya natsu suka fara amsawa.


Har zuwa na karshe wato;


Laaa ilaha illallah!


A lokaci ɗaya duk suka amsa da 

(laaa ilaha illallah Muhammadurrasulillah sallallahu alaihi wa salam, Allahumma rabba hazihida'awatit tammah, wassalatul qa'imah, aati Muhammadu Al wasilata Wal fadeelah, wa ba'athhu maqaman mahamuda Allazee wa'ad ta.

Allahumma Salli ala Muhammad wa'ala aali Muhammad, kama sallaita ala Ibrahim wa ala aali Ibrahim innaka hamidun majeed, wa barik ala Muhammad wa'ala aali Muhammad kama barakta ala Ibrahim wa ala aali Ibrahim innaka hamidun majeed)


"ya ke ƴar uwa shin kin san falalar amsa kiran sallah kuwa? Ko wani irin yanayi kike ko wani irin nauyi ne a gareki in har bakinki ze iya motsawa manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gareshi ya ce 'idan kuka ji me kiran sallah to ku faɗi irin abinda yake faɗi, sannan kuyi salati gareni, domin wadda yayi salati ɗaya a gareni Allah zai yi salati goma a gareshi".


Bayan an idar da isha duk gida kowa yayi anan aka fara haramar cin abincin dare, ita kam dae Fauza ko kallon inda su Fatima suke bata yi ba suma ba wadda ya mata magana saboda tuwo ne kuma miyan kuka ko shakureta ake ba ci zata yi ba.


Mp wadda kowa da kowa ke dashi personal a gidan me ɗauke da memory 32Gb cikinshi karatuttuka ne na malamai daban daban da kuma riwayoyi kala kala sede fa Fauza nata harda wakoki kala daban daban na mawaka mabanbanta, memoryn take cire wa ta kai school wata friend ɗinta ta saka a wayanta su tura wakoki duk ta harhardace rabi da kwata yanzu ma wakar Auta waziri na Kewa ta saka tana ji murya chan kasa kasa, Sam bata ji shigowar shi ba se jin kiran sunanta tayi cikin kaushin murya wadda ya sakata saurin mikewa tana zare idanu zuciyarta na bugawa, yau idan waƙar nan ne ya shiga kunne Baba ta shiga uku!....


DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. 

Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.

Acc no. 0545475847 

Acc name. Fatima Muhammad Gurin 

Bank name. Gt bank

Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin 

09039206763 

Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp.

Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰


Karku sake a baku labari.



               🖤Gureenjoh🖤

No comments