Breaking News

Diddigar Kaya 6


 DIDDIGAR ƘAYA 

   (Mai Wuyar Tsincewa)


بسم لله الرحمن الرحيم 


FATIMA MUHAMMAD GURIN.             

         (Gureenjo)


ADABI WRITERS ASSOCIATION 


Marubuciyar:

*Zuhraa*

*Hamrah*

*Igiyar Rayuwa*

*Noor Iman*

*Ruwan Sama..*

*Lelewal*

*GAMON JINI paid*

*Kowa Ya ga zabuwa..*

And Now..

*Diddigar ƙaya... Paid*


                 *Shafi Na Shidda*


*PAID BOOK*


ÆŠANÆŠANO


**WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI MRSJMOON GWANATA KUMA SHUGABATA🥰❤️**


"Wa'alaikumussalam warahmatullah sannu da zuwa Mammi"

Cewar Fauxa tana me sakin murmushi.


Jaddah ma sannu Da zuwa ta mata, Seda ta amsa na Jaddah kan tace 

"Fauxa ke kam ba zan amsa ba, riƙe kayan ki"


Dariya suka yi duka tace

"yi hakuri maa in shaa Allahu zan zo"


Tace 

"na gaji da ji, ke kam gidan mu kaman wadda aka yiwa farraku dashi idan ba'a compound ba ko nan sashen Jaddah ba'a ganinki Sam?"


Dariya kawai take yi, wlh ita tana rasa dalilin da yasa take kasa shiga sashen na Baba prof, duk matanshi ma dama banda gaisuwa Mammi ce kawai take sakewa sossai, tana son matan ba tare da ta san dalili ba.


"Ina yini Jaddah? Fatan mun sameku lafiya?"


Cike da so Jaddah ta amsa mata, duk cikin surukanta babu mafi soyuwa a gareta irin Aisha, matar ta dabance cikin mata, tana da kawaici sossai gata da fara'a bazaka taɓa ganinta bata murmushi ba, tana da son mutane da jan kowa a jiki bata damuwa da kai nata ne ko ba nata ba, tana da kirki fiye da zato, duk cikin matan na Baba prof babu me shiga kitchen da kanshi yayiwa Jaddah girki na musamman ya kuma tako ya kawo ya zauna suyi hira sossai irin Mammi.


Dukda tana yawan fama da matsanancin ciwon kafa se ta kwana biyu uku ma bata iya tafiya idan ciwon ya tasar mata amma hakan be sa tayi kasa a gwiwa wurin kula da mijinta da surukanta ba, kuma ita da kanta take taya baba prof kula da mahaifiyar tashi mace ce da a duk lokacin da mijinta ze shigo da wani abu a Leda bazata taɓa karɓa ba se ta tambayeshi ina na Jaddah? Idan har ya manta ko be saya ba sbd ganin ta girma da abun ko wani abu haka zata sa ya koma ya sayo, tana da wani ƙima na daban a zuciyar mutanen gidan musamman mijinta da surukuwarta.


"Aisha ya ciwon kafan? Fatan kin ji daaÉ—in maganin nan na Gamborun gala?"


Tana murmushi tace 

"wlh na ji daaɗinshi sossai Jaddah, kafa yayi sauƙi sosai"


Jaddah tace 

"Toh Allah ya qara afuwa"


Suka amsa da Ameen. 


Chan cikin hiransu Jaddah tace 

"ni kam Aisha kina ji daga wurin wannan Miskilin nawa kuwa? Kwana biyu be kirani ba fa"


Maa tace tana murmushi 

"eh Jaddah, ya ce min ze shiga ƙasar da bashi da simcard ɗinta idan har ze fi kwana biyu to ze saya Sim ɗin sbd mu ji lafiyar shi idan kuma ba ze wuce hakan ba in ya bar ƙasar in shaa Allah ze ƙira"


Jaddah tayi tsaki tace 

"ba ga irin ta ba, mutum ne kullum a sama kaman tsuntsu fisabilillahi idan ya zo nan fa ya zube Sima simai se ki dauka kamfanin mtn ne, wani idan ya manta na wace kasa ce kuma be da lokacin gwadawa sede kiji katttt ya karya ta"


Mammi na dariya zata yi magana kenan Fauxa ta miƙe Tsam tayi ɗakin Jaddah fuskanta babu yabo babu fallasa, da idanu duk suka bita Seda ta shige kan Jaddah ta zabga tagumi cikin jimami.


Mammi tace 

"Jaddah Dan Allah ki dena sa damuwa a ranki sbd yaran nan kar kije wani ciwo ya kama ki, har yanzu dukkansu yara ne in Shaa Allah gaba ko ance su yi baza su yi ba"


Jaddah tace 

"se yaushe kenan Aisha? Karki manta Faizan ya baiwa Talatin da biyar baya wannan ta fi sha shida amma ace se gaba? Wani gaban kuma bayan wannan? Wlh Allah ya gani babu abunda ke ci min tuwo a ƙwarya irin tsananin rashin jituwar yaran nan, har tsoro irin ƙin da suke yiwa juna yake bani kwata kwata ɗaya baze taɓa bada fuska ayi maganan ɗaya a gabanshi ba?"


Mammi tace 

"ni na fi ganin laifin shi babban kwabon nasu ai, na yi faÉ—a har na gaji amma ya kasa fahimtata"


Jaddah tace 

"ya Allah ka kawo mana karshen wannan abun nasu"


Mammi ta amsa da Ameen suka kama wani hiran kuma se dab magrib kowa yayi alwala suka tafi masallaci a tare.


Bayan kwana biyu


Tunda ta tsefe kanta bata yi kitso ba gashi har yau Sunday, barta dae da neman tsokananta wadda bata rabo dashi, ita da fa'iza ce tafe suna hira sbd duk gidan babu wacce suke shiri kuma suke ƙaunar juna kaman fa'iza babu wacce kuma ta tsana irin Fatima in ka cire Faizan.


Abun nata kaman jinnu, tana son fa'iza sbd haƙurin ta ta kan yi hakuri da duk wani halinta tana yawan kare ta, in kaga sun yi faɗa to akan Fatima ne, Fatima na son nuna mata uwarsu ɗaya da fa'iza ita kuma ta tsani hakan, idan kuma fa'iza tace mata kar ta biyewa Fatima su yi ai jinin dake yawo a jikinta shine yake yawo a nata jikin tunda uba suka Haɗa se ta ce ai fa'iza ta goyi bayan Fatima alhali Agola take a gidan Anan zasu yi faɗa su Rabu Toh Fauxa da zuciya se ayi kwana biyu bata huce ba hakan yasa shirin su da fa'izan yake yawan ja baya.


Sashen Jaddah suka shiga tana zaune tana jan chasbi Fauxa ta zube kan kujera tace 

"Jaddah wainar fulawa nake son ci na manja da yaji me tafarnuwa"


Jaddah tace 

"se ki ci ai, ni kam ban yi tunanin akwai fulawa a gidan nan ba"


Fa'iza tace 

"kash! Ya kenan Fauxa gashi namu ma babu ya kare"


Mikewa Fauxa tayi tace 

"mu je wurin Mammi mu yi, dama wlh tun jiya ban je na gaisheta da ciwon kafan nan nata da ya tashi ba"


Ficewa suka yi Jaddah bata ce komai ba har suka fice, ko da suka isa a ɗaki suka sameta kwance a ƙasa an shimfiɗa mata bargo me taushi da pillows, ƴar yayarta da zata ɗan girme su da take hannun ta tun bayan auren farida ita ke taimaka mata tunda bata karatu.


Sashukan nan basu da maraba da sashen su Fauxa, se na kitchen da akwai cikin kowanni sashe saɓanin nasu, se kuma na yawan ɗakuna wadda nan kofa biyu ke fuskantan biyu, na Mammi ne na farko wadda babban parlor ne sossai da kitchen da ɗakuna biyu, hakan ne kuma a kowanni ɗaki, sannan akwai kitchen na waje da kowacce me girki a sashen take girki ranan girkin ta, tsakar gidansu bishiyar cashew ce me ni'imtacciyar inuwa.


"Fauxa yau ke ce a sashen namu? Lallai za'a yi ruwa da kankara"


Fauxa na murmushi ta zube kasa tace 

"sannu Mammi ina yini? Ya kafa?"


Mammi tace 

"Alhamdulillah Fauxa da sauki sossai har É—azu ma na taka zuwa toilet"


Fauxa tace 

"Allah ubangiji ya ƙara sauki"


Da Ameen ta amsa, fai'za ma ta gaisheta.


Fauxa tace 

"Mammikina da fulawa? Wainar fulawa nake son yi bamu da fulawa haka Jaddah ma"

Ta karashe tana karya wuya


Mammi tace 

"Ah Kice abunda ya kawo ki kenan ba zuwa na musamman da kike cewa ba"


Tana dariya tace 

"Allah ba haka bane dama nayi niyyar zuwa"


Mammi tace

"ba za'a rasa fulawan nan ba ku duba a kitchen na cikin nan se kuyi, dama akwai yaji da Zuwaira(kanwar ta) ta kawo min ma jiya da alama ze yi daaÉ—i"


Cikin jin daaÉ—i Fauxa ta mike, fa'iza ta bi bayanta suka yi kitchen.


Anan suka kwaÉ“a suka fara suya se suka fara na manja sbd yadda Fauxa ta hanata sakat Seda suka yi me yawa se suka koma man gyaÉ—a sbd shi fa'iza ke so, suna cikin yi se Fa'iza tace 

"ni bani manjan ma in yi mixing kaÉ—an yadda ze bada wani dandano me armashi"


Fauxa tace 

"Wallahi bazan bayar ba ka jimin wayau, kowa ya ci da plain abunda yake so"


Musu suka fara, fa'iza ta kai hannu da niyyar fusgan manjan Fauxa ta É“alle da gudu daidai kofar kitchen É—in taji taci wani uban karo da wani broad chest me yanayi da rock, gabaÉ—aya manjan ya zube a jikin kayan mutumin.


A hankali na kai idanuna bisa mutumin da aka kwararawa manjan Masha Allah, kyakyawar matashi ne me tsawo sossai a kamannin fuska zaka iya cewa kaman an tsaga kara da Fauxa, banbancin nasu kaɗan ne shi ɗin fari ne Kal saɓanin Fauxa, haka idanunshi wasu irin Ash ne me walƙiya..


Ko kaÉ—an bashi da rama wani irin tsayayyen namiji ne da yake da jikin every woman dream, daga ka ganshi zaka san cewa ma'abocin workouts ne, yana da dogon hanci sak irin nata da lips wadda suke iri daya da nata kaman an shafa musu cherries yadda suke kyalli, yana da gashin saje gyararre me kyau wadda har zuwa gemu amma be cika yawa ba, a gyare tsab baÆ™i sidiÆ™ se shining yake yi wadda ya kara fitar da ainihin kalar farin fatar shi, daga yatsunshi na hannu zuwa na kafa dogaye ne a gyare suke tsab gwanin burgewa, yana da wani irin kwarjini da farin jini sede fa  ma'abocin tsare gida ne, Miskilin bugawa a jarida ne sannan yana da murÉ—aÉ—É—en hali da zama dashi se ka shirya.


Sanye yake da Fararen kaya Kal Kal Jean da shirt designers kafafunshi sanye da Dior lufas masu kyau, kamshinshi a take ya baza lungu da sako na kitchen É—in, kyawawan idanunshi na kafe kan inda manja ya zube a Rigan nashi kan a hankali cikin tsantsar natsuwa ya É—ago birkitattun idanunsa dake cike da kwarjini irin na cikakkun maza ya zuba mata.


Wani irin faɗuwar gaba ne ya risketa ga tsoro da ya kusa sumar da ita, cikin da na sanin fara sha'awar wainar fulawa da ta yi a yau ta fara ja da baya, wannan baƙin azzalumin yanzu se ya mata abunda se ta gwammaci kiɗa da karatu, ita kanta fa'iza dake tsaye jikin gas a take ta saukar da pan ɗin sede ta kasa kashe gas ɗin se rawan tsoro jikinta ya ɗauka.


Kokari yake yayi controlling É“acin ranshi sede ganin ko sannu bare yi haÆ™uri ta kasa ce mai yasa ya É—aga kafafunshi ya fara takawa zuwa gareta, a duniya ya tsani ganin yarinyar halayen ta, neman tsokananta, rashin jinta, rashin kunyarta duk ya tsana bata  yi mishi don babu fuskan yi É—in sede ya kan tsinkaya tana yiwa wasu, sannu be taÉ“a HaÉ—a su ba tana karama in har zata zo kusa dashi se ya mata mugunta tun tana zuwa har ta dena hakan ya dasa mata tsoron shi, Sam baya zama a inda take sbd hakan itama ta koyi kin zama a inda yake, idan kana son ganin É“acin ranshi ka ce suna kama yanzu se ku samu matsala, ya kan yi mamakin yadda kowa a gidan complain É—inshi baya wuce Fauziyya har iyayensu maza,  shi yana ganin iskancinta wuri ya samu bata sami me saita ta bane, hakan ya sa ya buga Mata tambarin annoba don shi da annoba yake kiranta. 


Ganin da gaske nufanta yake ga fuskanshi babu ɗigon rahama yasa tayi kokarin gudu, taku ɗaya yayi ya saka mata ƙafa hantsilawa tayi zata faɗi, garin neman abunda zata dafe don gujewa kaiwa ƙasa ta ɗaura hannunta na dama bisa kan gas ɗin da yake kunne, ba wutan bane karafunan da suka riga suka jima da ɗaukan zafi sossai ne suka aika mata da wani irin raɗaɗin azaba zuwa kwakwalwanta har bata san sadda ta saki wani ƙaran azaba ba tana rike hannun.


Wani mugun murmushi da ko haƙorin shi be bayyana ba ya saki kan ya juya ya fice daga kitchen ɗin, da gudu Fa'iza ta kashe gas ɗin kan tayi kanta ta kama hannunta a tsorace tana kallon fuskanta yadda hawaye ke ambaliya kaɗai zaka gani ka san tana cikin wani hali ga zufa dake aikin tsatsafo mata.


"Sannu Fauxa! Sannu"


Mammi ce jin ihun Fauxa yasa ta lallaɓa ta fito a hankali ta nufe su tana cewa

"Subhanallah me ya same ta? Konewa tayi?"


Cikin kuka Fauza tace 

"mammi wannan azzalumin ne ya saka min hannu akan karafunan gas, Wayyoooo hannuna!"


A hankali Mammi tace

"FAIZAN!" Don shi kaÉ—ai Fauxa ke cewa Azzalumi.

Da sauri Mammi ta cewa Fauxa 

"É—auko akamu yi sauri gashi a chan in saka mata kar ya tashi"


A hankali ta karasa gareta ta É—aga ta tare da riÆ™e hannun har ya tashi gabaÉ—aya tafin na hannunta yayi wani kalar bororo, wani irin tausayinta ne ya rufe Maa sbd ta san zafin wuta ba daaÉ—i amma se ta saÉ“awa Faizan, ashe kaddarar Æ™one wa ya kawo ta sashen nata da ta jima tana mita akan rashin zuwan nata, da kuwa ta san Faizan ma ze zo yau da bata ma bari sun yi wainar anan ba, wani irin abu ne haka? 


Akamun fa'iza ta kawo ta kwaɓa ta saka mata har lokacin kuka take, tayi tayi ta ci wainar da saura kaɗan ma su kammala ta ƙi tace ta koshi, cikin rashin jin daaɗi Mammi ke bin ta da ido har ta fice se ta saka fa'iza juye wainar a flask ta bita dashi su je su ci a gida don ta tabbatar ko sashen Jaddah Fauxa bazata kara zuwa ba se an tabbatar mata da baya gari.


Haka kuwa aka yi da fa'iza ta kawo mata ma ƙin ci tayi, Allah ya isa kuwa ta ja mishi yayi cikin kwando, gashi Ammin ta bata nan ta tafi kauyensu jiya uncle ɗinta ya rasu, da magrib ma da kyar ta samu tayi alwala ta tako zata fito zuwa masallaci kenan ta tsaya Chak jin muryar dake tashi a speaker na masallacin, tsaki ta ja ta koma ɗaki nan tayi sallah har isha bata fita ba, a Cewar ta bazata bi sallar azzalumi ba don Allah ba karba ze yi ba. bayan tayi isha ne ta kunna speaker ɗinta iya daidai jin kunnen ta ta saka waƙa abunta anan mood ɗinta ya fara dawowa daidai.


Tana ji su fai'za na cin abinci bata fita ba, idanunta a lumshe take jin Fatima na fesawa fa'iza ita duk yadda take jin karatu bata taɓa jin me natsuwa da kwantar da hankali irin na Ya Faizan ba, fa'iza na dariya tace mata


"zaki ce haka ne ma tunda kina son shi"

Fatima ta ce 

"ban gane ina son shi ba? Ko de muna son juna?"


Fa'iza tace 

"ai ko makaho ya shafa ya san ke ce kike mahaukacin son ya Faizan shi ba take yake ba, ba ta yadda za'a yi yana son ki ne ke karan kanki kan ya miki magana É—aya se kinyi hamsin, sannan ya tafi yayi wata da watanni ko a wayan Jaddah baze ce a baki ku gaisa ba idan ma yana jin kunyar Mammi kenan, ni wlh bana son miki kasancewa da ya Faizan ina so ki samu me son ki inda zaki ji...."


Tsawa ta daka mata

"dakata fa'iza! Don ina maganan soyayyata dake ba shi yake nufin ki gayamin duk wani banzan maganan da ze fito daga bakin ki ba idan ma ba kitsa miki aka yi ba don baki da wannan wayaun, to henceforth as from today kika kara min irin wannan maganan wlh se nayi mummunan saɓa miki ni ba sa'ar ki bace"


Fa'iza tace 

"Ya Fati daga faÉ—ar gaskiya?"


"Bana son gaskiyar ki riƙeta"


Daidai lokacin Fakiha ta shigo da gudu tana shelan ya Faizan ya ce a je a karɓi tsaraba yana sashen Jaddah.


Da sauri duk suka tashi suka fice daga tsakar gidan.


Taɓe baki Fauxa tayi, Fatima na neman magananta ta tabbatar harda shagube a zancen nata, amma ba ta ita take ba yanzu ta samu ta warke shine damuwanta kuma wlh akan Fatima zata rama abunda ya mata tunda shi azzalumin ya fi karfinta.


Chan da yunwa ya fara damunta don ko abincin rana bata ci ba ta sa a zuciyarta zata ci wainar fulawa yasa ta mike ta fito a hankali ta nufi kitchen, ja tayi ta tsaya jin kuka na tashi a hankali....


DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuÉ—i ne.. 

Ze zo muku a Naira É—ari uku kachal #N300.

Acc no. 0545475847 

Acc name. Fatima Muhammad Gurin 

Bank name. Gt bank

Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin 

09039206763 

Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp.

Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰


Karku sake a baku labari.



               ðŸ–¤Gureenjoh🖤

No comments